Daga: Ahmed Ilallah
Katsinawa na Dikko dakin kara, kamar yadda a ke yi musu kirari. Shugaba Tinubu ma yace ammasa kara da nishaɗantarwa, yace ya ji kamar a kurmin Lagos yake.
Tabbas wannan ziyara ta Shugaba Tinubu ta tarihi ce, domin ita ce jaha ta farko da ya ziyarta tun zamansa Shugaban Ƙasa har ya kwana, banda mahaifar sa ta Lagos.
Wannan ziyara, tunda a ka ambata yinta hankalin duk wani mai kishin Nijeriya da Arewacin Nijeriya ya koma kanta, ganin yadda wannan jaha ta ke cikin bala’in rashin tsaro, wanda ba ta taɓa fuskanta ba a tarihin jihar da makwabtanta irin su Zamfara, Sokoto da Kebbi.
Kusan dai a yanzu babu wani abun da Katsinawa ke buƙata da ya kai a kakkaɓe musu ƴanta’addar da suka mamaye dazukansu, suka hanasu noma, neman abinci da walwala ta ɗan’adam kamar yadda mutanen Legos da Port Harcourt suke ciki.
WANI LABARIN: Gwamnatin Jigawa Za Ta Tantance Masu Karɓar Fansho Don Tabbatar Da Gaskiya
Amma a bun da yafi ɗaukar hankali a wannan ziyara, ganin kawai banbaɗanci na ƙoƙarin jawo gobe ko wunin yau ɗin ma ba a san ya za a kai shi ba.
Ba ƙoƙarin yaya za a yi Tinubun ya sauƙe nauyin da ke kansa na samar da tsaro a Katsina da sauaran Arewacin Nijeriya ba, a matsayin babban bala’in da ya sako mu a gaba ba, wai babanɗancin sai ya yi tazarce a 2027 a ke.
Nishaɗantarwa, a bin da ya sake tabbata a wannan ziyara, shine gamsuwar da Shugaba Tinubu ya yi na cewa an nishaɗantar da shi, tamkar a Kurmin Legas.
Kash, shin shugabannin nan sun manta da bala’in da Katsinawan ƙauye suke ciki ne, na yaƙi da azabtarwar da ƴanfashin daji ke musu.
A tunanin duk wani wanda ya fahimci siyasar duniya shine, nunawa shugaba masifar da jihar ta ke ciki, da kuma jan hankalin shugaba a kan ya yi duk mai iyuwa don ceto jihar Katsina shi ya dace a fifita.
Zaman lafiya da samar da tsaro dai, shine kaɗai zai ba da tabbacin yin noma da bunƙasa noma a wannan jiha ta Katsinawa, kuma ya ba wa masu zaɓe yaƙinin yin ma zaɓen a kakar baɗin.
alhajilallah@gmail.com