Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Shettima Da Shugabannin Afrika Sun Halarci Rantsar Da Sabon Shugaban Gabon, Brice Nguema

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima tare da sauran shugabannin ƙasashen Afirka sun halarci bikin rantsar da sabon shugaban Gabon, Brice Nguema, wanda ya gudana ranar Asabar a filin wasa na Stade de l’Amitié sino-gabonaise da ke Libreville.

Mr Nguema ya zama shugaban ƙasar ne bayan da ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na ranar 12 ga Afrilu 2025, inda ya doke ƴantakara bakwai.

Kafin wannan lokaci, Nguema na riƙon gwamnati na tsawon watanni 20 bayan sauke Ali Bongo daga mulki.

WANI LABARIN: RIKICIN SUDAN: Rundunar RSF Ta Kai Farmaki Filin Jirgin Sama Tare Da Wani Wurin Ajiyar Makamai

A wajen bikin, an gudanar da gangamin sojoji da gagarumin nune-nunen al’adun Gabon domin nuna haɗin kai da alfahari da asalin ƙasar.

A jawabinsa na rantsuwa, Nguema ya ce: “Ina godiya ga jama’ar ƙasa bisa irin goyon bayan da suka bani wanda ya kai ni wannan matsayi ta hanyar dimokuraɗiyya.”

Ya yi alƙawarin samar da cigaba mai ɗorewa, da ƙarfafa matasa da gyara matsalolin rashin tsaro da ƙarancin ruwan sha.

Ya ƙara da cewa zai yi aiki da Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma miƙa buɗaɗɗen kiran haɗin kai tsakanin ƙasashen Afirka, inda ya ce: “Zamunci da zaman lafiya ne ginshiƙin ci gaban Afirka baki ɗaya.”