Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) ta bayyana cewa sun dakatar da shirin mamaye ofisoshin jam’iyyar Labour Party (LP) a faɗin ƙasa ne domin ba hukumar zaɓe INEC damar nazarin hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara da ta yanke a watan jiya.
Shugaban Kwamitin Siyasa na NLC, Farfesa Theophilus Ndubuaku, ya ce: “Muna jiran INEC ta gama nazarin kwafin hukuncin kafin mu ɗauki mataki, domin dimokuraɗiyya tana buƙatar haƙuri da bin doka.”
WANI LABARIN:
Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya bayar da umarni a ranar 9 ga Afrilu cewa a fara shirin mamaye ofisoshin LP guda 36 da hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja, bisa zargin cewar shugabannin jam’iyyar na ƙin bin hukuncin kotu.
A cewarsa, “Ba za mu zauna ba mu yi komai ba, muna kallon yadda Abure da tawagarsa ke keta hukuncin kotu.”
Sai dai kakakin LP, Obiora Ifoh, ya ce barazanar NLC wata hanya ce ta neman ɓata sunan jam’iyyar a idon INEC da jami’an tsaro.
Yayin da wasu ke ganin shirin na NLC ya mutu, Ndubuaku ya ce: “A’a, ba mu dakatar da shirin ba. Muna jiran matakin INEC ne kawai, saboda abin ya shafi dimokuraɗiyyar ƙasa da kuma abin da duniya ke kallo.”