Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Shugaban NSCDC Ya Yaba Da Aikin Tsaro A Jigawa Yayin Ziyartar Gwamna Namadi

Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya karɓi baƙuncin Babban Kwamandan Hukumar Tsaro ta Ƙasa (NSCDC), Dr. Ahmed Abubakar Audi, a safiyar Lahadi a fadar gwamnati da ke Dutse, a wani ɓangare na zagayen aikin da shugaban hukumar ke yi a shiyyar Arewa maso Yamma.

Dr. Audi, wanda ya isa tare da manyan jami’an hukumar daga Abuja, ya yaba da jajircewar Gwamna Namadi wajen aiwatar da muhimman ayyukan ci gaba da suka bayyana jihar a matsayin abin koyi a ƙasa baki ɗaya.

Ya bayyana cewa, “Gwamna Namadi yana daga cikin shugabannin da suka sanya ayyuka a gaba fiye da hayaniya, kuma al’ummarsa na amfana da hakan kai tsaye.”

WANI LABARIN: Kusan Duk Mazauna Karkara A Najeriya Na Rayuwa Ne Cikin Talauci – Bankin Duniya

Bugu da ƙari, shugaban NSCDC ya miƙa ta’aziyyarsa ga gwamnan bisa rasuwar mahaifiyarsa da ɗansa, inda ya roƙi Allah Ya ji ƙansu Ya ba da haƙuri.

A nasa ɓangaren, Gwamna Namadi ya gode wa Dr. Audi bisa wannan ziyarar mai cike da ƙima, yana mai cewa irin hakan wata alamar nagartaccen shugabanci ce da nuna kishin ƙasa.

Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da bai wa dukkan hukumomin tsaro haɗin kai don tabbatar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Wannan na cikin matakan da gwamnatin ke ɗauka domin tabbatar da ci gaban jihar cikin aminci da kwanciyar hankali, a cewar Malam Garba Al-Hadejawy, mai taimaka wa gwamna ta ɓangaren sabbin kafafen sadarwa.