Kungiyar Ƴan Uwa Masu Kishin Auyo (ACCF) ta bayyana fargabar yuwuwar ƙara tabarbarewar tsaro a Auyo da kewaye yayin wani taron tattaunawa da suka gudanar kan al’amuran tsaro a yankin, inda suka nuna cewa yankin da aka sani da noma tun fil’azal yanzu na fuskantar barazana daga miyagu da ke ƙoƙarin hana samar da amfanin gona da lalata ci gaban da ake samu.
A cikin jawabin da Babban Sakataren ƙungiyar, Zakar Tukur, ya fitar, ya bayyana cewa yanzu haka manoma ba sa iya kai ziyara gonakinsu bayan faɗuwar rana ko zirga-zirga a hanyoyin zuwa gonaki ba tare da fuskantar barazana ga rayukansu ba, inda aka sha sace injinan ban ruwa da sauran kayan aikin gona har ma da ƙwace motocin wasu.
Ya ce, “Wannan yanayi na iya janyo koma-baya ga noman shinkafa da yankin ke alfahari da shi a faɗin ƙasa, wanda kuma zai iya yi wa jihar illa a matsayin ɗaya daga cikin manyan jihohin da ke samar da shinkafa.”
WANI LABARIN: Shugaban NSCDC Ya Yaba Da Aikin Tsaro A Jigawa Yayin Ziyartar Gwamna Namadi
Ƙungiyar ta nuna damuwa kan ƙarancin jami’an tsaro da kayan aiki da ke kawo cikas wajen magance matsalar, inda ta buƙaci matakin gaggawa daga hukumomi kafin lamarin ya ƙazanta kamar yadda aka gani a wasu jihohin kamar Zamfara da Katsina.
Daga cikin shawarwarin da suka bayar akwai kafa kwamitin sintiri na haɗin gwiwa, ƙayyade zirga-zirgar mutane da makamai, da yin rajistar dukkan baƙi a ƙarƙashin sarakunan gargajiya.
Sauran matakan sun haɗa da tallafa wa masu kula da tsaro da kayan aiki, da kuma ƙara himma wajen addu’a da tsare-tsare na hana yaɗuwar barazana.
Ƙungiyar ta roƙi dukkan hukumomi da masu ruwa da tsaki su ɗauki matakin gaggawa domin kare lafiyar al’umma da tabbatar da zaman lafiya a Auyo da jihar Jigawa baki ɗaya.