Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Su Wanene Masu Son Zama Fafaroma Bayan Fafaroma Francis?

A cikin makon nan, cardinal-cardinal daga sassa daban-daban na duniya za su hallara a Vatican domin fara aikin zaɓen sabon Fafaroma, wanda zai maye gurbin marigayi Fafaroma Francis, wanda aka yi masa jana’iza ranar 26 ga Afrilu.

Zaɓen da ake sa ran farawa bayan 7 ga watan Mayu zai gudana ne a cikin sirri a dakin Sistine Chapel, inda ba za a ba da damar amfani da waya, intanet ko fita daga ciki ba, har sai an fidda sunan sabon shugaban cocin Katolika.

Wannan zaɓe, wanda aka fi sani da “conclave,” wani al’amari ne mai cike da tarihi da muhimmanci ga mabiyansa miliyan 1.4 a duniya baki ɗaya.

Kafin zaɓen, cardinal-cardinal za su gudanar da taruka na musamman da ake kira congregazioni, domin tattaunawa kan irin shugaba da suka ke bukata; duk da cewa daga cikin su 252, mutum 135 kacal ne za su iya kada ƙuri’a – waɗanda shekarunsu ba su kai 80 ba.

Duk da kasancewar babu wanda ke kamfe a fili, Roberto Regoli, masanin tarihin cocin Katolika daga Jami’ar Pontifical Gregorian ta Roma, ya ce “Aiki ne mai wahala, ba ka da lokacin kanka.”

A cewar Miles Pattenden daga Jami’ar Oxford, “Francis ya kasance mutum mai hanzari, amma yanzu cocin na iya neman wanda zai fi taka-tsantsan.”

WANI LABARIN: Shugabannin CPC Sun Ce Suna Yin APC Ne Kawai Saboda Buhari, Duk Da Cewa An Mayar Da Su Saniyar Ware

Zaɓen na da matuƙar ƙalubale saboda yawan bambance-bambancen ra’ayi da aƙida da ke tsakanin kadinal-kadinal – wasu masu ra’ayin sauyi ne yayin da wasu suka fi karkata zuwa gargajiya.

Daga cikin waɗanda ake hasashen na iya zama Fafaroma akwai Cardinal Luis Antonio Tagle daga Philippines, wanda ake kira “Asian Francis,” saboda irin salon jinkansa; Cardinal Pietro Parolin daga Italiya, wanda ke da ƙwarewa a harkokin diflomasiyya; Cardinal Peter Turkson daga Ghana, wanda ke da matsakaiciyar akida; da kuma Cardinal Erdo daga Hungary, wanda ya fi karkata ga ra’ayin mazan jiya.

Har ila yau, akwai Matteo Zuppi wanda ya taka rawa a zaman lafiya tsakanin Ukraine da Rasha, da Fridolin Besungu daga Kongo, wanda ke nuna kishin al’ada, da Michael Czerny daga Canada, wanda ke jagorantar ayyukan adalcin zamantakewa.

Cardinal Pierbattista Pizzaballa, shugaban cocin Katolika a Urushalima, na ɗaya daga cikin matasa masu ƙwarewa a rikicin Gabas ta Tsakiya, yayin da Cardinal Robert Sarah daga Guinea ke da goyon bayan masu ra’ayin gargajiya.

Regoli ya kara da cewa, “Wanda zai zama Fafaroma dole ne ya iya daidaita tsakanin tsarkaka da shugabanci mai sanin makamar aiki.”

Alamar hazo fari daga cikin chimney a Sistine Chapel ita ce zata tabbatar da cewa an zaɓi sabon Fafaroma, yayin da hazo baki ke nuna ba a cimma matsaya ba.