Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Akwai Babbar Illa Tattare Da Barin Waya Kusa Kai Yayin Yin Bacci, In Ji Wani Masani

Akin Ibitoye, wani mai ba da shawara kan fasaha a kamfanin TMB Tech, ya yi gargaɗi mai ƙarfi ga ƴan Najeriya da su guji barci da wayar hannu a ƙarƙashin matasansu ko a gefen gadonsu, yana mai cewa hakan na da illa ga lafiyar jiki da hankali.

A cikin wata hira da aka yi da shi a Morning Brief na Channels Television a yau Litinin, Ibitoye ya bayyana cewa amfani da na’urorin sadarwa a lokacin bacci yana dagula tsarin bacci na jiki da kuma haifar da haɗari, ciki har da fashewar batirin wayar.

“Kada ka kwanta da wayarka a ƙarƙashin matashinka. Idan kana bacci da ita a ƙarƙashin matashi, tana shafan ka ne, kai ba ka ma sani ba,” in ji shi.

Ya bayyana cewa fitila mai shuɗin haske daga wayoyi na iya dagula tsarin jikin mutum na circadian rhythm wanda ke da alhakin daidaita lokutan bacci da farkawa bisa ga haske da sauyin yanayi.

WANI LABARIN: Su Wanene Masu Son Zama Fafaroma Bayan Fafaroma Francis?

Ibitoye ya ƙara da cewa: “Waɗannan na’urori na iya dagula tsarin baccinka, saboda haka idan dare ya yi, jiki yana samun saƙo na yin bacci. Idan ba ka samu isasshen bacci ba, masana kiwon lafiya sun tabbatar da cewa hakan na iya janyo illa ga lafiyar ka.”

Ya kuma ce saɓanin tsoffin agogon ƙararrawar tashi, wayoyin hannu suna jan hankali da pop-up da girgiza, kuma mutane da dama suna faɗawa cikin doomscrolling, inda mutum ke yunƙurin dubawa na ɗan lokaci sai ya ɗauki awanni.

“Mun tattauna kan doomscrolling, inda mutum ke shirin duba Instagram na mintuna biyar amma ya ɗauki sa’o’i biyu,” in ji shi.

Ya shawarci mutane da su koma amfani da agogon tashi maimakon dogaro da wayar hannu domin gujewa wannan matsala, yana mai cewa: “Kafin wayar hannu, muna amfani da agogon tashi ne kawai wanda ba zai ƙara ba sai lokacin ya yi.”