Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Gwamnatin Tarayya Za Ta Magance Rikicin Manoma da Makiyaya A Jigawa – Sanata Malam Madori

Daga: Yaseer Mika’il, Dutse

Gwamnatin tarayya ta kammala shirin kafa rundunar ‘yan sanda masu tarwatsa tarzoma a karamar hukumar Guri ta jihar Jigawa domin rage rikice-rikicen da ke faruwa tsakanin manoma da makiyaya, kamar yadda sanata mai wakiltar Jigawa Arewa maso Gabas, Abdulhamid Ahmed Malam-Madori ya bayyana yayin taron Gwamnati da Jama’a na gwamnatin jihar da aka gudanar a Guri.

Sanata Malam-Madori ya ƙara da cewa za a gina sabbin barikin ƴansanda guda ashirin a yankin tare da ofishin ƴansanda mai hawa ɗaya wanda za a sanya masa na’urorin tsaro na zamani, a haɗin gwiwar gwamnatin tarayya da ta jihar Jigawa.

“Wannan wani ɓangare ne na ƙoƙarin haɗin gwiwa tsakanin gwamnatocin jiha da tarayya don tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa, musamman tsakanin makiyaya da manoma,” in ji shi.

WANI LABARIN: Kusan Dukkan Ɗaliban Da Suka Rubuta JAMB Ta Bana Sun Gaza Samun Rabin Makin Jarabawar

Ya bayyana Guri a matsayin ɗaya daga cikin yankunan da suka fi albarka da filayen noma masu faɗin gaske, inda ake samun damina da noman rani sau biyu a kowace shekara, lamarin da ke jawo makiyaya daga wajen Najeriya, wanda hakan ke haddasa saɓani da manoma.

“Tsohuwar gwamnati ba ta mai da hankali sosai ba kan wannan matsala, amma gwamnatin Malam Umar Namadi ta fito da tsare-tsare da dama da ke bai wa kowane ɓangare haƙƙinsa, wanda hakan ke ƙara kwanciyar hankali a yankin,” in ji shi.

Har ila yau, Sanatan ya ce za a fara gina filin wasa na zamani a Guri ranar Juma’a 9 ga wannan wata, wanda zai kasance da manyan allunan kallo da fasahar zamani domin bai wa matasa da tsofaffi damar kallon wasannin ƙwallon kafa na gida da na waje.

Ya kuma bayyana cewa fiye da matasa 40 daga yankin sun samu ayyukan gwamnati a hukumar ƴansanda, soja, kwastam da shige da fice, ciki har da wata mace lauya da yanzu haka ke aiki da hukumar kula da ayyukan ƴansanda.