Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Mutane Da Dama Sun Mutu A Bauchi Bayan Wani Faɗa Tsakanin Ƴanbanga Da Ƴanbindiga

A ƙalla mutane 25 sun rasa rayukansu sakamakon arangama mai zafi tsakanin wasu ƴanbanga da ƴanbindiga a ƙauyukan ƙaramar hukumar Alkaleri ta jihar Bauchi, inda aka tabbatar da mutuwar ƴanbanga tara, ƴanbindiga biyar, da kuma waɗanda ba su ji ba ba su gani ba 11 da aka sace daga yankin kafin a hallaka su, kamar yadda DAILY TRUST ta rawaito.

A cewar kakakin ƴansanda na jihar, CSP Ahmed Wakil, “a ranar 4 ga Mayu, 2025, misalin ƙarfe 9:40 na safe, rundunar ƴansanda ta samu rahoto daga ofishinta na Alkaleri kan wani farmaki da aka kai wa ƴanbanga da ke sintiri a dajin Duguri da ke iyakar Bauchi da Plateau.”

Wakil ya ce “a lokacin da ƴanbanga daga yankunan Duguri da Gwana ke kan sintiri, sai wasu ƴanbindiga suka musu kwanton-ɓauna a Dajin Madam, wanda ya haifar da arangama mai muni.”

WANI LABARIN: Rikici Ya Ɓarke A Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma Kan Tallafin Karatu

Shaidun gani da ido kamar Malam Isa Muhammad sun bayyana cewa “ƴanbindigar sun kai hari ne bayan sun sace mutane 16 da shanu 500 daga wani ƙauye, kuma ƴanbanga suka bi sawunsu har suka yi artabun.”

Wani ɗan banga da ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce, “mambobinmu huɗu daga ƙauyukan Duguri, Kajigamu da Yelwan Duguri sun rasa rayukansu,” sannan akwai wasu da suka fito daga Plateau da ƙauyen Mansur.

Gwamna Bala Mohammed ya bayyana jimamin sa da takaici, inda a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan yaɗa labarai Mukhtar Gidado ya fitar, ya ce, “wannan mummunan hari da aka kai wa jaruman matasanmu da ke kare al’umma, wata alamar haɗari ce da ke ci gaba da barazana ga zaman lafiya da tsaro.”

Gwamnan ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan da suka rasa ƴan’uwa da dukan al’ummar Alkaleri da jihar Bauchi baki ɗaya, yana mai tabbatar da ƙudirin gwamnatinsa na ganin an gurfanar da waɗanda suka aikata wannan mummunan laifi.