Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da wani kwamiti na musamman domin yin cikakken nazari kan tsarin hidimar ƙasa ta matasa (NYSC), tare da gabatar da sabbin shirye-shiryen gyara da za su dace da buƙatun zamani da na ƙasa baki ɗaya.
Ministan Ci gaban Matasa, Ayodele Olawande, ne ya sanar da haka a ranar Talata a Abuja yayin bikin ƙaddamar da kwamitin.
A cewarsa, “Yau rana ce mai muhimmanci a cikin ƙoƙarinmu na ci gaba da inganta ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin ƙasa da ke da alaƙa da haɗin kai, ƙarfafawa da ci gaban matasa.”
Ministan ya bayyana cewa NYSC ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da haɗin kai a tsakanin al’ummomin Najeriya tun bayan kafuwarta a shekarar 1973, amma lokaci ya yi da za a sake duba tsarin domin ya dace da ƙalubalen da ake fuskanta a yanzu.
WANI LABARIN: Ƴan Birnin Na Ƙwace Gonakin Ƴan Ƙauye Yayin Da Tsanani Ke Sa Talakawa Ɗiban Guntun Injin Niƙa Don Abinci A Najeriya
“Dole ne mu gyara muhimman cibiyoyin da ke tallafawa ci gaban ƙasa yayin da muke cigaba da tafiya gaba,” in ji shi.
Ya bayyana wasu daga cikin matsalolin da tsarin ke fuskanta, ciki har da rashin tsaro ga masu hidima, giɓin kayan aiki da kuma tambayoyi kan dacewar tsarin da yanayin tattalin arziki da zamantakewa na yanzu.
Mr Olawande ya ce an bai wa kwamitin umarnin yin cikakken bincike kan tsarin, duba ayyukansa na yanzu da kuma gabatar da shawarwari domin inganta tsarin ta hanyar ingantaccen tsaro, ƙirƙire-ƙirƙire da ingantaccen tasiri.
Ya ce, “Burinmu shi ne mu mayar da NYSC wata kafa ta musamman da ke bai wa matasa damar koyon sana’o’i, ƙarfafa harkar kasuwanci, shiga harkokin jama’a da kuma samar da ci gaban aiyuka.”