Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Ɗaliban Polytechnics Sun Bai Wa NELFUND Kwana Biyar Don Fitar Da Bayanai Ko Ta Fuskanci Zanga-Zanga

Ƙungiyar Ɗaliban Polytechnics Najeriya (NAPS) ta bai wa hukumar bayar da bashin ɗalibai ta ƙasa (NELFUND) wa’adin kwana biyar domin fitar da cikakken bayani kan yadda aka rarraba bashin ɗaliban kwalejoji, bisa zargin rashin gaskiya a tsarin.

Wannan ƙorafi na zuwa ne a yayin da ake ƙara bayyana damuwa kan yadda ake tafiyar da shirin bayar da bashin, inda hukumar NOA ta zargi wasu cibiyoyi da haɗin guiwar bankuna wajen cire kuɗaɗe ba bisa ƙa’ida ba daga asusun ɗalibai.

Rahoton da PUNCH ta rawaito ya nuna cewa hukumar ICPC ta bayyana cewa daga cikin Naira biliyan 100 da NELFUND ta raba, an tabbatar da amfani da Naira biliyan 71 kacal, abin da ya janyo fushin jama’a da kuma zanga-zangar ɗalibai a babbar hanyar Legas zuwa Ibadan a ranar Litinin.

WANI LABARIN: Utomi Ya Ƙaddamar Da Gwamnatin Bayan Fage Don Ƙalubalantar Gwamnatin Tinubu

A cikin wata sanarwa da shugaban NAPS, Eshiofune Oghayan, da shugaban majalisar dokokin ƙungiyar, Oyewumi Ayomide, suka sanya wa hannu, ƙungiyar ta gargaɗi NELFUND da ta fitar da takamaiman adadin da ya nuna yadda ɗaliban polytecnics suka amfana daga tallafin.

“Mun bai wa hukumar NELFUND wa’adin kwana biyar da ta fitar da cikakken bayani kan yadda aka raba bashin, da adadi da sunayen waɗanda suka amfana a kwalejojin fasahar,” in ji sanarwar.

Haka kuma ƙungiyar ta ce idan hukumar ta kasa, za su farkar da ɗalibai don gudanar da zanga-zanga tare da kai ƙara ga hukumar DSS da EFCC don gudanar da bincike.

“Za mu bi duk wata hanya ta dimokuraɗiyya domin neman adalci idan an ci gaba da ɓoye gaskiya,” in ji sanarwar kamar yadda PUNCH ta rawaito.