Majalisar Dattijai ta Najeriya a ranar Laraba ta amince da dokoki biyu daga cikin dokokin gyaran haraji huɗu da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya gabatar, a wani mataki da ke zama muhimmin cigaba wajen sauya tsarin tattara haraji na ƙasa.
Dokokin da aka amince da su sun haɗa da “Nigeria Revenue Service Establishment Bill” da kuma “Joint Revenue Board Establishment Bill”, waɗanda suka zo kwana guda bayan jinkirta zaman majalisa domin sake duba muhimman sassan dokokin.
Sai dai majalisar ta yi watsi da ƙudurin ƙara harajin VAT daga kashi 7.5 cikin ɗari zuwa kashi 10 cikin ɗari, bisa la’akari da tsadar rayuwa da ke ci gaba da sa ƴan ƙasa cikin ƙunci.
WANI LABARIN: Ɗaliban Polytechnics Sun Bai Wa NELFUND Kwana Biyar Don Fitar Da Bayanai Ko Ta Fuskanci Zanga-Zanga
Tinubu ya aike da dokokin haraji huɗu ne gaba ɗaya tun a watan Oktoban 2024, a wani yunƙuri na inganta tattara haraji da kuma kula da kuɗaɗen jama’a.
Bayan nazari na tsawon sa’a biyu a rahoton kwamitin da Sanata Sani Musa ke jagoranta, shugaban majalisar dattijai Godswill Akpabio ya bayyana amincewa da dokokin tare da yabawa ƴan majalisar.
“Waɗannan dokokin za su canza yadda ake gudanar da harkokin haraji a Najeriya. Ina godiya da jajircewar ku wajen samar da wannan muhimmin kundin doka,” in ji Akpabio.
Sanata Barau Jibrin, mataimakin shugaban majalisar dattijai, ya yaba da irin haɗin kan da aka samu duk da rashin jituwar da aka samu a farko inda ya ƙara da cewa, “Rikici a irin waɗannan batutuwa abin al’ada ne, amma mun daidaita komai cikin hikima.”