Kwamishinan ƴansanda na Jihar Edo, Monday Agbonika, ya bayyana cewa rundunar ta cafke mutane 95 da ake zargi da shiga ƙungiyoyin asiri tare da gurfanar da su a gaban kotu a cikin watan farko na aikinsa.
Kamar yadda jaridar PUNCH ta rawaito, kwamishinan ya ce an kuma ƙwato bindigogi 25 da suka haɗa da AK-47 guda biyu, harsasan roba 130, harsasai masu kisa 135, da kuma motoci huɗu da aka sace ko aka ƙwace da ƙarfi.
Sauran abubuwan da aka ƙwato sun haɗa da bindiga irin ta Lar Mark, bindigogin Ingila guda uku, bindiga Beretta guda ɗaya, da kuma bindigogin ƴan farauta guda huɗu, tare da kuɗi da wayar iPhone 16 Plus.
WANI LABARIN: Minista Ya Koka Kan Yunƙurin Samar Da Wutar Lantarki Da Makamashin Nukiliya A Najeriya
Agbonika ya bayyana hakan ne a taron manema labarai domin cika wata guda a kujerarsa, inda ya ce an ceto mutane bakwai daga hannun masu garkuwa da mutane, kuma mutane 12 da ake zargi da garkuwa sun bayyana sabuwar dabara da suke amfani da ita wajen tserewa da waɗanda suka kama.
“Masu garkuwa da mutane suna amfani da waɗanda suka kama a matsayin garkuwa lokacin da jami’an tsaro suka taso musu, wanda hakan ke hana mu buɗe musu wuta saboda jin tsoron kashe waɗanda ake garkuwa da su,” in ji shi.
Ya ce rundunar na aiki wajen samar da sabbin fasahohi don gano waɗannan miyagu ba tare da cutar da waɗanda aka sace ba.
Kwamishinan ya kuma sha alwashin ci gaba da haɗin gwiwa da al’umma, masu sintirin daji, da kuma dabarun wayar da kai don daƙile aikata laifuka, tare da haɗin gwiwar gwamnati wajen gyara tsarin ƴanbanga don tabbatar da cewa suna aiki ne kawai a yankunansu.