Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Indiya Ta Ja Kunnen Pakistan, Ta Yi Barazanar Mayar Da Martani Mai Zafi

Ministan harkokin wajen Indiya, S. Jaishankar ya bayyana cewa ƙasarsa ba ta da “niyyar tayar da fitina” da Pakistan, amma idan har aka kai musu hari, babu shakka za su mayar da zazzafan martani.

Jaishankar ya yi wannan furuci ne yayin wani babban taron haɗin gwiwa da ya gudana a birnin Delhi, wanda ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya halarta, a lokacin da Indiya da Iran ke bikin cika shekaru 75 da fara ƙawance.

A baya, Iran ta nemi shiga tsakani a rikici tsakanin Indiya da Pakistan, sai dai wannan ƙarin bayani daga Indiya na nuna cewa ƙasar ba za ta lamunci wata barazana ba.

WANI LABARIN: Robert Prevost, Ɗan Amurka Na Farko Ya Zama Sabon Fafaroma

“Indiya na son zaman lafiya, amma muna da ƙarfaffar kariya idan aka kai mana hari,” in ji Jaishankar.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da zaman ɗarɗar a yankin Kashmir da rikice-rikice bi-da-bi ke ci gaba da faruwa tsakanin dakarun Indiya da na Pakistan.

Masana diplomasiya na ganin wannan jawabi na iya ƙara dagula dangantakar diplomasiya a yankin.

A yanzu haka dai, ana fatan manyan ƙasashen duniya za su taka rawa wajen rage wannan tashin hankali mai yiwuwar iya rikiɗewa zuwa babban rikici.