Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Bill Gates Ya Ce Zai Rabawa Al’umma Dukkan Dukiyarsa Kafin Ya Rufe Gidauniyarsa

Fitaccen attajirin nan duniya kuma mai bayar da agaji, Bill Gates, ya bayyana shirin raba kusan dukkan dukiyarsa da ta kai dala biliyan 200 zuwa al’umma, inda zai bar kashi daya kacal (1%) domin kansa da iyalinsa, tare da sanar da cewa gidauniyarsa, Bill and Melinda Gates Foundation, za ta rufe aiki kwata-kwata ranar 31 ga watan Disamba, 2045.

Gates ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na intanet, Gates Notes, inda ya ce, “Mutane za su ce abubuwa da dama a kaina idan na mutu, amma bana so su ce ya mutu da arziƙi.”

Ya ƙara da cewa, “Akwai matsaloli masu buƙatar gaggawa da yawa da suka fi cancanta da wannan dukiya fiye da in ci gaba da riƙe ta.”

Gates ya bayyana cewa zai hanzarta rabawa al’umma dukiyarsa fiye da yadda ya tsara tun farko, inda ya ce, “Zan raba dukiyata ta hanyar gidauniyarmu cikin shekaru 20 masu zuwa domin aiyukan ceto da kyautata rayuka a duniya, sannan a 2045, gidauniyar za a rufe ta baki ɗaya.”

WANI LABARIN: Isra’ila Ta Kashe Fararen Hula 92 A Gaza, Ciki Har Da Ƙananan Yara

A wani hoto da ya wallafa a shafinsa, Gates ya bayyana shirin raba kashi 99% na dukiyarsa kafin wa’adin, ya bar kashi 1% wanda ya kai dala biliyan 1.6 ga kansa da ƴaƴansa, Phoebe, Rory da Jennifer.

Gidauniyar da ya kafa tare da tsohuwar matarsa, Melinda French Gates a shekarar 2000, ta kashe fiye da dala biliyan 100 wajen temakon kiwon lafiya, ilimi da yaƙi da talauci, ciki har da samar da rigakafi da taimakon gaggawa.

Gates ya ce sun taka rawa wajen ƙirƙiro rigakafin cutar rotavirus, wanda ya rage mace-macen yara sakamakon gudawa da kaso 75%.

Duk da nasarorin da gidauniyar ta samu, wasu na sukar ikon da Gates ke da shi a harkokin lafiya na duniya, amma a hirarsa da Associated Press, ya ce yana da ƴancin zaɓar inda zai kashe kuɗinsa.