Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Bankin Duniya Ya Kara Arawa Najeriya Dala Miliyan 215 Don Bayar Da Tallafi Ga Talakawa

Bankin Duniya ya sake fitar da ƙarin dala miliyan 215 ga Najeriya a ƙarƙashin shirin National Social Safety Net Programme–Scale Up wanda aka amince da shi tun daga Disamba 2021, lamarin da ya kai adadin kuɗin da aka fitar zuwa dala miliyan 530 daga cikin dala miliyan 800 da aka ware gaba ɗaya.

Rahoton da jaridar The PUNCH ta wallafa ya nuna cewa Bankin Duniya bai bayyana ranar fitar da kuɗin ba, amma ya sabunta bayanai a shafinsa na yanar gizo inda ya nuna hakan ya faru ne a cikin watan Mayu 2025.

Tun da fari, shirin na da nufin bayar da naira dubu biyar ga talakawa, amma gwamnatin Tinubu ta sauya tsarin zuwa biyan naira dubu 25 na tsawon watanni uku ga gidaje miliyan 15 domin rage raɗaɗin cire tallafin fetur.

WANI LABARIN: Bill Gates Ya Ce Zai Rabawa Al’umma Dukkan Dukiyarsa Kafin Ya Rufe Gidauniyarsa

Duk da wannan cigaba, Najeriya ta ci gaba da biyan kuɗaɗen ruwa kan lamunin tun kafin fara amfana da shi, inda aka kashe fiye da dala miliyan 6.18 wajen biyan ruwan bashin a shekarar 2024 kaɗai.

A watan Janairu da Yuli na shekarar 2024, an biya haraji iri-iri da suka haɗa da dala miliyan 1.81 da kuma fiye da dala miliyan 5.36, duk da cewa kaso mai yawa na kuɗaɗen bai shiga aikin kai tsaye ba saboda matsalolin shugabanci da cin hanci a ma’aikatar walwalar jama’a.

Tsohuwar Ministar Walwala, Sadiya Umar-Farouq, da kuma magajiyarta Dr Betta Edu duk an tsare su bisa zargin karkatar da kuɗaɗen tallafin, inda EFCC ta ce ta karɓo kusan Naira biliyan 32.7 da dala dubu 445 daga hannunsu da abokan aikinsu.

Gwamnati ta kafa kwamitin bincike ƙarƙashin Ministan Kuɗi, Wale Edun, domin sake fasalin tsarin bayar da tallafi tare da tabbatar da gaskiya wajen bayar da kuɗaɗen tallafi, yayin da Bankin Duniya ya ci gaba da bayyana matsayin aiwatar da shirin a matsayin “mai matsakaiciyar gaskiya,” yana mai cewa akwai gagarumin ƙalubale a fannin kula da kuɗi, saye da sayarwa, da kuma bibiyar aikin bayar da tallafin.