Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Ma’aikatan Internship a Asibitin Koyarwa na Tarayya, Gombe, Za Su Tsunduma Yajin Aiki Saboda Rage Musu Albashi da Jinkirin Biya

Wasu daga cikin masu aikin neman ƙarin ƙwarewa (interns) a Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Gombe sun sanar da fara yajin aiki daga ranar 19 ga Mayu, 2025, bisa zargin rashin biyan albashi, jinkirin biyan kuɗaɗe, da kuma cire musu kuɗi ba tare da wani bayani ba.

A wata sanarwa da suka fitar mai ɗauke da sa hannun ƙungiyar “Concerned Interns,” sun bayyana cewa “rashin bayyana dalilin cire kuɗaɗen da kuma rashin cika alkawarin da aka yi na biyan su ya jefa su cikin ƙuncin rayuwa a wannan mawuyacin lokaci na tattalin arziƙi.”

Sun ce “tuni wannan matsala ta janyo musu damuwa, rashin kwanciyar hankali, da kuma taɓarɓarewar harkokin rayuwar yau da kullum.”

Ma’aikatan sun bayyana cewa tun daga watan Disamba na shekarar 2024 ne suka fara lura da cewa “abin da ke cikin takardun albashinsu bai dace da abin da ake biyansu ba.”

KARANTA WANNAN MA: Bankin Duniya Ya Kara Arawa Najeriya Dala Miliyan 215 Don Bayar Da Tallafi Ga Talakawa

Sun ƙara da cewa, bayan sun kai koke, an shaida musu cewa “harajin watannin Nuwamba, Disambar 2024 da kuma Janairun 2025 ne aka cire duk daga albashin Disamba guda ɗaya.”

Duk da cewa an yi musu alƙawarin cewa “tsarin zai gyaru a watan Janairun 2025,” sai dai sun ce lamarin ya ƙara taɓarɓarewa, inda kuɗaɗen da ake biyansu ke ci gaba da raguwa ba tare da wata hujja ba.

“Yanzu takardun albashinmu na nuna sabon mafi ƙarancin albashi ake biyanmu, amma abin da muke samu ya fi na da ƙanƙanta,” in ji su.

Sun bayyana rashin amincewarsu da irin wannan rashin gaskiya, inda suka ce “ya kamata mu san a fili yanda albashinmu yake da dalilin duk wani canji da aka samu.”

A dalilin haka, sun ce ba su da wani zaɓi illa shiga yajin aiki domin kare ‘yancinsu da jin daɗinsu a wajen aiki.

Sun buƙaci “a bayyana dalilin duk wani ragin albashi kuma a tabbatar da cewa ana biyan albashi a kan lokaci ba tare da ɓata lokaci ko nuna wani fifiko ba.”

Wannan yajin aiki dai zai gudana ne a harabar Asibitin Koyarwa na Tarayyar da ke Gombe daga misalin ƙarfe 12:00 na dare a ranar Litinin.