Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Jigawa Ta Rage Bashin Da Ke Kanta Da Kaso 96% Yayin Da Gwamnatin Tarayya Da Jihohi 33 Ke Rage Basussukan Da Ke Kansu

A wani sauyi da yake zama abin yabawa a fagen kuɗi da mulki, gwamnatin tarayya tare da jihohi 33 da babban birnin tarayya sun fara wani gagarumin shirin rage bashin cikin gida da ake binsu, inda suka biya jimillar Naira Tiriliyan 1.85 daga watan Yunin 2023 zuwa ƙarshen shekarar 2024, lamarin da aka danganta da yawaitar kuɗaɗen shiga da sauye-sauyen tattalin arziƙin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, musamman cire tallafin mai da buɗe kasuwar canjin kuɗi.

A cewar Hukumar Kula da Bashi ta Ƙasa (DMO), jimillar bashin cikin gida na jihohi da FCT ya ragu daga Naira Tiriliyan 5.82 a watan Yunin 2023 zuwa Naira Tiriliyan 3.97 a ƙarshen 2024.

Jihar Delta ce ta fi biyan bashi, inda ta rage sama da rabin bashinta cikin watanni 18, daga Naira Biliyan 465.4 zuwa Naira Biliyan 199.58 bayan biyan Biliyan 265.83.

Sauran jihohi da suka biya bashin sama da Biliyan 60 sun haɗa da Lagos (Biliyan 96.2), Imo (Biliyan 94.7), Cross River (Biliyan 85.9), Ogun (Biliyan 81.3), Akwa Ibom (Biliyan 77.4), da Oyo (Biliyan 72.5).

Amma abin mamaki shi ne Jihar Jigawa wadda ta rage bashinta da kashi 96% daga Biliyan 43.13 zuwa Biliyan 1.33 kacal, yayin da jihar Ondo ta biya Biliyan 61.6 cikin Biliyan 74 da ake binta.

Duk da haka, jihohin Rivers, Enugu da Neja ba su rage bashinsu ba, maimakon haka sun ƙara ciwo bashi cikin wannan lokacin, inda jihar Rivers ta ƙara yawan bashin da ke kanta da Biliyan 138.89.

WANI LABARIN: Hukumar NiMet Ta Bayyana Yanda Yanayi Zai Kasance Daga Lahadi Zuwa Talata A Najeriya

A ɓangaren gwamnatin tarayya, ta biya dala biliyan 7 na bashin waje cikin watanni 18 na mulkin Tinubu, ciki har da biyan dukkan bashin da IMF ke bi daga dala biliyan 3.26 a Yunin 2023 zuwa sifili a zango na biyu na 2025.

Wannan ci gaba ya sa alaƙar Najeriya da IMF da Bankin Duniya ta ƙaru, yayin da jimillar bashin cikin gida ya ci gaba da raguwa.

Gwamnatin tarayya ta daina karɓar “Ways and Means” daga Babban Bankin Najeriya, inda ta koma kasuwar hada-hadar kuɗi domin ɗaukar nauyin giɓin kasafi, kuma ta biya bashin Sukuk na farko da aka fitar tun 2018.

A shekarar 2024 kaɗai, gwamnatin tarayya ta kashe Naira Tiriliyan 5.87 domin biyan bashin cikin gida, wanda ya ninka abin da gwamnatin baya ta kashe a 2022.

Wannan sabuwar manufa ta ba da damar ganin ƙarancin giɓin kasafin kuɗi da rage dogaro da bashi, wanda ke nufin ƙarin kuɗi ga ayyukan raya ƙasa.

A hannu guda, FAAC ya ba wa jihohi da ƙananan hukumomi Naira Tiriliyan 9.58 a 2024, wanda ya ninka na shekarar 2022 da kaso 28.6%.

Wannan ya ba da dama ga jihohi su ɗauki nauyin kasafinsu ba tare da ciwo bashi ba.

“Bailout” wanda ya zama ruwan dare a gwamnatin baya, yanzu ya zama tarihi yayin da jihohi ke biyan basussukansu da kansu ba tare da ƙorafi ko yajin aiki ba duk da ƙarin mafi ƙarancin albashi daga Naira 30,000 zuwa 70,000.

Ministan Kuɗi Olawale Edun ya ce, “Waɗannan matakai sun samar da sabuwar rayuwa ga jihohi da gwamnati gaba ɗaya,” yana mai cewa tsarin ya samar da isasshen kuɗi da zaman lafiya a harkar kuɗi.

Wannan ya nuna cewa sauye-sauyen tattalin arziƙin Tinubu ba kawai maganganu ba ne, “sai dai sabbin ginshiƙai na ɗorewar kuɗi a Najeriya,” a cewar Ministan Kasafi da Tsare-Tsare, Atiku Bagudu.