Gidauniyar Baba Azimi Foundation (BAF) tare da hadin gwiwar shirin Local Rights Programme (LRP) a ƙarkashin tsarin Inclusive Forum for Accountable Society (IFAS), ta shirya taron bayan watanni uku-uku na yini daya domin duba nasarorin da aka samu da kuma tsara matakai na gaba.
Taron wanda aka gudanar a dakin taro na Ma’aikatar Harkokin Mata da ke sabuwar sakateriyar Jihar Jigawa a Dutse, ya samu goyon bayan ActionAid Nigeria tare da halartar wakilan al’umma, hukumomin gwamnati, kungiyoyin fararen hula da ƴan jarida.
Da take jawabi a taron, shugabar IFAS Barrista Aisha Sulaiman ta bayyana cewa “shirin LRP yana gudana ne ta hanyar wannan taron tare da tallafin ActionAid domin magance matsaloli a wasu al’ummu da aka zaɓo”.
KARANTA WANNAN MA: TASHIN BAMA-BAMAI: Ƴan Boko Haram Sun Hallaka Fasinjoji 9 A Borno
Ta ƙara da cewa al’ummomi bakwai ne daga ƙananan hukumomi uku na jihar Jigawa ke cin gajiyar shirin, ciki har da Duwigi, Dan Abzin, Rakwata Sale, Rakwata Ado, Girtigini, Sabara da Aigwan Iro.
Taron ya baiwa mahalarta damar tattauna batutuwan da suka shafi ilimi, karancin ruwan amfani, ƙarfafa mata da kiwon lafiya, da kuma tantance irin nasarori da ƙalubalen da aka fuskanta.
Haka kuma, an sake nazartar irin tasirin da yunƙure-yunƙuren neman sauye-sauye da aka yi a matakin jiha suka yi wajen tallafa wa ci gaban al’ummomin da ke karkashin shirin na LRP.
A ƙarshe, mahalarta taron sun bayyana godiya ga Baba Azimi Foundation da ActionAid bisa wannan tsari tare da alƙawarin ci gaba da bayar da haɗin kai domin samun ƙarin nasarori da ci gaba a yankunan da abin ya shafa.