Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

NiMET Ta Fitar Da Hasashen Samun Ruwan Sama Da Guguwa Daga Litinin Zuwa Laraba A Sassan Najeriya

Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya, wato NiMet, ta fitar da rahoton hasashen yanayi na kwanaki uku daga Litinin zuwa Laraba, inda ta ce ana sa ran samun guguwar iska da ruwan sama a sassa daban-daban na ƙasar.

A cikin bayanin da aka fitar ranar Lahadi a birnin Abuja, NiMet ta ce “sassan Taraba, Kaduna, Gombe, Bauchi, Kebbi, Sokoto, Katsina, Jigawa da Kano za su fuskanci ruwan sama da guguwa da sassafe a ranar Litinin.”

Bayan haka, hukumar ta bayyana cewa ana sa ran ci gaba da ruwan sama da guguwar iska a yammacin ranar a jihohin Taraba, Kaduna, Sokoto, Borno, Kebbi da Zamfara.

A yankin Arewa ta Tsakiya kuwa, NiMet ta ce “za a samu ruwan sama da guguwa da safe a Jihohin Abuja, Neja da Nasarawa,” sannan da yamma ana sa ran hakan zai ci gaba a Plateau, Abuja, Nasarawa, Kwara, Neja, Kogi da Benue.

A yankin Kudu, ana hasashen ganin sararin sama mai gajimare da yuwuwar samun ruwan sama da safe a Ondo, Ogun, Edo, Ebonyi, Abia, Cross River, Rivers da Akwa Ibom.

KARANTA WANNAN MA: Fusatattun Ma’aikatan Shari’a Sun Garƙame Babbar Kotun Tarayya Ta Abuja Yayin Fara Yajin Aiki

Har ila yau, hukumar ta ce a yammacin ranar, “ana sa ran samun ruwa a jihohin Oyo, Ekiti, Ogun, Osun, Ondo, Lagos, Edo, Abia, Imo, Ebonyi, Enugu, Anambra, Akwa Ibom, Cross River, Rivers, Delta da Bayelsa.”

A ranar Talata kuma, za a fuskanci irin wannan yanayi da safe a jihohin Kano, Zamfara, Katsina, Bauchi, Gombe, Adamawa, Borno, Yobe da Taraba, yayin da za a ci gaba da ruwa da guguwa a jihohin Taraba, Kebbi, Borno, Gombe, Adamawa, Kaduna, Bauchi da Katsina a yammacin ranar.

“Za a sami ruwan sama da guguwa a Arewa ta Tsakiya da safe, musamman a Abuja, Neja da Nasarawa,” sannan daga bisani a ci gaba da ruwa a Nasarawa, Kogi, Neja, Kwara da Plateau.

A ranar Laraba kuwa, hukumar ta hasashen yanayi ta ce ana sa ran samun guguwar iska da ruwa a Zamfara, Adamawa, Kaduna, Sokoto, Kebbi da Taraba da rana, da kuma a Kaduna, Katsina, Bauchi, Zamfara, Sokoto da Adamawa a yammacin ranar.

Hukumar ta ce “a lokacin da ake sa ran ruwan saman, ana iya fuskantar ƙaruwa ko ƙarfi a guguwar iska, don haka jama’a su ɗauki matakan kariya.”

Ta shawarci mutane su “cire na’urorin lantarki daga soket, su guji tsayuwa kusa da manyan itatuwa da kuma guje wa tuƙi a lokacin ruwan sama mai ƙarfi.” Haka kuma, “kamfanonin jiragen sama su riƙa samun rahoton yanayi na musamman daga NiMet domin tsara tashi da sauƙar jirage yadda ya dace,” in ji hukumar.

Ta kuma jaddada cewa “jama’a su kasance masu bin shafin yanar gizon NiMet a http://www.nimet.gov.ng domin samun sabbin bayanai kan yanayi.”