Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Saudiyya Ta Hana Fiye Da Mutane 269,000 Shiga Birnin Makka Don Aikin Hajjin Bana

Hukumomin Saudiyya sun hana mutum 269,678 shiga birnin Makka ba tare da lasisin aikin Hajji ba a wani ƙoƙari na hana cunkoso da tabbatar da tsaro yayin babban aikin Hajjin bana, kamar yadda rahotanni daga AlArabiya da Associated Press suka bayyana jiya Lahadi.

Ma’aikatar Cikin Gidan Saudiyya ta bayyana cewa wannan mataki ya shafi ƴan kasa da mazauna Saudiyya da ke ƙoƙarin gudanar da Hajji ba bisa ƙa’ida ba.

A cewar jami’an tsaro, waɗanda suka karya wannan doka za su fuskanci tara har ta dala 5,000 da kuma yiwuwar karɓar ƙorafi daga ƙasar.

Haka kuma, an hukunta fiye da mazauna birnin su 23,000 bisa karya dokokin Hajji tare da janye lasisin masu ba da hidimar Hajji guda 400.

WANI LABARIN: Wike Ya Ce Babu Wanda Ya Isa Ya Kore Shi Daga PDP, Yayin Da Kiraye-Kirayen Korarsa Ke Tayar Da Kura

A wani taron manema labarai a birnin Makka, Laftanar Janar Mohammed al-Omari ya ce, “Mahajjaci yana kan idonmu, kuma wanda ya saɓa doka, yana hannunmu.”

Wadannan matakai na tsaurara doka sun biyo bayan damuwa kan haɗarin da ke tattare da mahajjatan da ba su da rajista, musamman waɗanda suka mutu a lokacin zafin rana na bara.

Yanzu haka, kusan mahajjata miliyan 1.4 da ke da izini sun isa Makka, kuma ana sa ran ƙarin mahajjata za su ƙaraso cikin kwanaki masu zuwa.

A wannan shekarar an fara amfani da jiragen sama marasa matuki (drones) wajen duba taron, gudanar da sintiri da kuma kashe gobara a matsayin sabon mataki na fasaha don inganta tsaro.

Aikin Hajji dai na ɗaya daga cikin ginshiƙan Musulunci guda biyar da ke wajaba ga duk Musulmi da ya cika sharuɗan lafiya da hali.

Sai dai zafin rana da ake fuskanta a bana ya ƙara ɗaga hankalin hukumomi da likitoci game da lafiyar mahajjata.