Rahoton sabuwar ƙididdiga daga hukumar UBEC ya nuna cewa malamai 915,913 ne ke koyarwa a makarantu 131,377 na matakin firamare a Najeriya, duk da cewa adadin ɗalibai ya haura miliyan 31 – lamarin da ke nuna babban giɓi da ke barazana ga ingancin ilimi.
Wannan matsalar na faruwa ne a daidai lokacin da malamai a birnin tarayya Abuja suka tsunduma yajin aiki saboda rashin aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta amince da shi tun a bara.
Binciken jaridar The PUNCH ya kuma nuna cewa jihohi 18 ba su ɗauki sabbin malamai ba tsakanin 2019 zuwa 2024, wanda hakan ke ƙara dagula halin da ake ciki.
WANI LABARIN: IMF Ta Buƙaci Najeriya Ta Ƙarawa Ƴan Ƙasa Haraji, Ta Kuma Inganta Tsarin Kasafin Kuɗi Don Rage Talauci
Hukumar Rajistar Malamai ta Ƙasa (TRCN) ta bayyana damuwa kan wannan matsala, inda tsohon shugabanta, Farfesa Josiah Ajiboye, ya ce “yawan yara da ke shiga makaranta da ƙarancin sabbin malamai na haifar da nauyin da makarantu ba za su iya ɗauka ba.”
Rahoton ya nuna cewa makarantu da dama, musamman a yankunan karkara, ana samun malami ɗaya ko biyu ne da ke kula da ɗalibai da dama, abin da ke haifar da matsalar talaucin koyo (learning poverty).
Shugaban ƙungiyar malamai ta ƙasa, NUT, Titus Amba, ya ce: “Wasu makarantun ana gudanar da su da malami ɗaya kacal, inda ɗalibai ke cikin halin rashin makoma mai kyau.”
Ya yi kira ga gwamnati a matakai daban-daban da su ɗauki matakin gaggawa wajen ɗaukar ƙwararrun malamai, yana mai cewa “kowane ɗalibi na da haƙƙin samun malamin da ya cancanta.”