Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

An Buƙaci Samar da Takardar Shaidar Kammala Karatun Almajirai Domin Ba Su Damar Ci Gaba da Karatu

An yi kira ga Hukumar Kula da Ilimin Almajirai da Yara Marasa Zuwa Makaranta (National Commission for Almajiri and Out-of-School Children Education) da ta samar da wata doka da za ta ba wa ɗaliban da suka haddace Alƙur’ani mai girma takardar shaida, domin su samu damar ci gaba da karatu har zuwa matakin jami’a da kuma cin gajiyar damarmakin gwamnati.

Wannan kiran ya fito ne daga Mai Martaba Sarkin Machina, Alhaji (Dr.) Bashir Albishir Bukar Machinama (OON, L’ONN), Shugaban Kwamitin Amintattu na Ƙungiyar Darul Naharatul Ahbabul Qur’an ta Najeriya, yayin wata ziyara ta musamman da ya kai wa Babban Sakataren Hukumar, Alhaji Dr. Sani Muhammad Idris, a ofishinsa da ke Abuja.

Dr. Bashir, ya bayyana takaicinsa kan rashin la’akari da tsarin ilimin almajirai a cikin Dokar Ilimi ta Ƙasa, yana mai cewa hakan yana hana almajirai damar ci gaba da karatu ko neman muƙamai a zaɓe.

Ya ce, “Dokar Kundin Tsarin Mulki ta Najeriya tana buƙatar takardar kammala sakandare a matsayin mafi ƙarancin ƙwarewa ga duk wanda zai tsaya takara, lamarin da ke nuna wariya ga waɗanda suka haddace Alƙur’ani.”

Sarkin ya buƙaci a samar da dabaru da za su ɗauki ilimin almajirai a matsayin wata sahihiyar hanya ta samun ilimi kamar sauran ilimai.

WANI LABARIN: Shekara Ɗaya Bayan Hukuncin Kotun Ƙoli, Gwamnatin Tarayya Ta Gaza Tabbatar Da Ƴancin Ƙananan Hukumomi

Ya bayyana muhimman ɓangarorin aikin ƙungiyarsu, kamar ziyartar makarantu domin tantance yanayin rayuwar almajirai, wayar da kai kan tsafta da zaman lafiya, sauya tsarin koyarwa, koyar da sana’o’i da kuma kawar da bara.

A nasa ɓangaren, Alhaji Dr. Sani Muhammad Idris ya yaba da ayyukan ƙungiyar, yana mai kiran haɗin gwiwa tsakanin hukumar da ƙungiyar don inganta rayuwar almajirai, musamman a Arewacin Najeriya.

Ya ce, “Muna aiki kan buɗe makarantu masu koyar da ilimin Alƙur’ani da kuma horar da ɗalibai yadda za su ci gaba da karatu har jami’a.”

Ya bayyana cewa Ministan Ilimi ya riga ya bayar da umarnin tattara bayanai domin tsara sabon tsarin ilimin almajirai, wanda a cewarsa, yana dab da kamala a yanzu.

Babban Sakataren ya umarci Shugaban Sashen Ilimin Almajirai da ya duba shawarwarin ƙungiyar kuma ya kafa kyakkyawar alaƙa da su.

Haka kuma, ya tabbatar wa da ƙungiyar cewa hukumar za ta tallafa musu a ci gaba da ayyukansu, musamman wajen shawo kan matsalar barace-barace.

Ya ƙara da cewa hukumar na shirin samar da tsarin ciyar da almajirai kamar yadda ake yi a makarantu na zamani.

“Wannan zai taimaka wajen daidaita tsarin almajiri da tsarin ilimin gwamnati,” in ji shi.

Dr. Bashir ya sake jaddada buƙatar gyaran da zai ba da dama ga almajirai su shiga tsarin ilimi da kuma zamantakewar ƙasar gaba ɗaya.

A ƙarshe, ya roƙi masu ruwa da tsaki da su ɗauki matakin da ya dace domin tabbatar da cewa ilimin Alƙur’ani yana da daraja daidai da na sauran fannonin ilimi a Najeriya.