Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Tsadar Taki Na Hana Noman Shinkafa Da Masara A Najeriya A Bana

Wasu manoma a Najeriya, musamman na shinkafa da masara, na bayyana damuwa kan yiwuwar fuskantar asara saboda tashin gwauron zabi na farashin taki da sauran kayan aikin gona.

Wasu daga cikin su ma sun hakura da noman shinkafar baki ɗaya, inda suka koma noman wasu kayayyaki kamar gero, dawa, riɗi da rogo.

Duk da da’awar gwamnatin tarayya na cewa ta rage farashin takin zamani domin tallafa wa manoma, da yawa daga cikin su na ci gaba da ƙorafi kan rashin iya siya a farashin da ake samu a kasuwa.

Alhaji Muhammad Idris, wani manomi daga jihar Jigawa, ya shaida wa BBC Hausa cewa ya kashe sama da naira miliyan ɗaya da dubu ɗari takwas wajen siyan taki da yin ban ruwa.

WANI LABARIN: DA ƊUMI-ƊUMI: Sanata Natasha Ta Kutsa Cikin Zauren Majalisa Duk Da Yunƙurin Hanata Shiga

“Duk da kuɗin da na kashe, gaskiya babu riba idan aka yi la’akari da farashin da ake sayar da shinkafa a yanzu,” in ji shi.

A cewarsa, idan aka noma shinkafa a hekta guda, ana iya samun buhu 40 zuwa 60, amma kuɗin da ake kashewa yana hana samun riba ga manomi.

Rahotanni daga sassa daban-daban na ƙasar na nuni da cewa manoma sun koma wasu nau’ikan noma don tsira da kai.

Alhaji Idris ya buƙaci gwamnatin Najeriya ta dawo da tallafin taki da kuma samar da maganin ciyawa domin sauƙaƙa rayuwar manoma.

Ya ce hakan ne kaɗai zai sa harkar noma ta ɗore kuma ta bai wa manoma damar yin noma mai nutsuwa da riba.