Ɗan jam’iyyar APC kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Adamu Garba, ya zargi wasu makusantan Shugaba Bola Tinubu da ɓoye masa gaskiyar halin da ƙasa da jam’iyyar ke ciki, yana mai cewa su na yaudararsa da cewa komai na tafiya lafiya.
A wata tattaunawa da ya yi da Channels Television a shirin Politics Today, Adamu ya bayyana cewa “Ina ganin akwai mayaudara a kusa da shugaban ƙasa; suna gaya masa abubuwan da ba su dace ba, gaskiyar ita ce abubuwa ba sa tafiya daidai.”
Ya ce sauyin siyasa da ya biyo bayan murabus ɗin Abdullahi Ganduje daga shugabancin jam’iyyar APC ya bai wa ƙawancen jam’iyyun hamayya da ke ƙarƙashin ADC damar shigowa da ƙarfinsu.
WANI LABARIN: Yara 400,000 Zasu Mutu Nan Da Ƙasa Da Kwana 40 Saboda Yunwa A Najeriya
“Su dai suna jiran faɗuwarmu ne, kuma wannan ne ya sa dole mu zama masu gaskiya a kanmu,” in ji shi.
Adamu ya yi gargaɗin cewa shugabanci a jam’iyya na buƙatar mutum mai gaskiya wanda zai saurari suka da kyakykyawan nufi ba tare da jayayya ko yin yabo na banza ba.
Ya kuma bayyana cewa rashin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari a siyasa ya haifar da giɓin da ke ƙara dagula lissafin APC a Arewacin Najeriya.
“Tun kafin rasuwarsa, adadin ƙuri’un arewa ya ragu, domin a zaɓen 2023 APC ta samu ƙuri’u miliyan 5.5 ne kawai daga arewa, alhali a baya Buhari na samun miliyan 12,” in ji shi.
Duk da haka, ya ce nasarar APC a 2023 ta samu ne bisa tsarin da aka gina da dabarun da aka tsara tun farko.
Adamu Garba ya kammala da cewa “abinda muke buƙata yanzu shi ne sake samar da tsari cikin natsuwa domin tafiya da tsarin siyasa na gaba ba tare da dogaro da Buhari ba.”