Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Yadda Gwamna Namadi Ke Kiyaye Daidaito Tsakanin Masarautun Jigawa

Tun bayan ƙirƙirar jihar Jigawa daga tsohuwar jihar Kano a 1991, zaɓen Dutse a matsayin babban birni maimakon Hadejia ya janyo taƙaddama mai tsawo tsakanin masarautu.

Rikicin ya fito fili a zaɓen 2023 lokacin da APC ta zaɓi Umar Namadi daga Hadejia a matsayin ɗan takarar gwamna da Engr. Aminu Usman daga Gumel, wanda wasu daga masarautar Dutse suka ƙi amincewa da su.

Sai dai a cikin makon farko bayan rantsar da shi, Gwamna Namadi ya naɗa manyan muƙamai kamar sakataren gwamnati daga masarautar Dutse domin kawo daidaito.

A wata ziyara da Sarkin Dutse, Hamim Nuhu Sanusi, ya kai masa a watan Maris, ya yaba da ayyukan da gwamnatin ke yi a masarautar.

WANI LABARIN: Ƴan Jigawa Na Adawa Da Yunƙurin Gwamnati Na Gina Shaguna Kan Naira Biliyan 3.5 A Kano

“Ba ƙaramar godiya ba ce, domin ayyukan ruwa, hanyoyi, gidaje da lafiya sun shafi kowane ɓangare na masarautar,” in ji sarkin.

Sarki Hamim ya ce aikin ruwa da ake yi yanzu da tallafin bankin duniya wanda ke da kuɗi naira biliyan 10.8 yana kawo sauƙi a harkar noma da zamantakewa.

Abdulhamid Sani, wani matashi daga Dutse, ya ce shirin samar da titi mai tsawon kilomita 15 a kowace shekara yana nuna irin hangen nesa da gwamnan ke da shi.

“Wannan ba gina hanya ba ce kawai, a’a, yana sauya rayuwar birni zuwa wajen samun arziƙi da haɗin kai,” in ji shi.

Tsohon gwamna, Muhammad Badaru Abubakar, wanda a yanzu shine Ministan Tsaro, ya ce ayyukan Namadi sun tabbatar da cewa ya zaɓi mutumin da ya dace a matsayin magajinsa.