Gwamnatin tarayya ta bayyana shirinta na bayar da tallafin Naira miliyan 50 ga daliban da ke karatu a fannoni na kimiyya, fasaha, injiniya, lissafi da likitanci (STEMM) a manyan makarantu domin bunƙasa ƙirƙire-ƙirƙire da kasuwanci a tsakanin matasa.
Wannan shiri mai suna Student Venture Capital Grant (S-VCG), na da nufin samar da damar kasuwanci ga ɗalibai domin gina masana’antu masu ɗorewa da samar da ayyukan yi a ƙasa.
A cewar wata sanarwa daga daraktar yaɗa labarai da hulɗa da jama’a ta ma’aikatar ilimi, Folashade Boriowo, an shirya ƙaddamar da shirin a watan Agusta, ƙarƙashin jagorancin Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa.
WANI LABARIN: Kotu Ta Yankewa G-Fresh Hukuncin Ɗauri Bisa Cin Zarafin Naira
An bayyana hakan ne yayin wani taron haɗin gwiwa da ya haɗa da shugabannin jami’o’i da kwalejoji, shugabannin ɗalibai, malamai da ƙungiyoyin ci gaba, domin samun matsaya wajen bunƙasa ƙirƙire-ƙirƙiren da ɗalibai za su jagoranta.
Tallafin zai mayar da hankali ne kan ɗaliban da ke karatu daga matakin ajin 300 a fannoni na STEMM, inda kowanne mai nema zai iya samun tallafi har zuwa Naira miliyan 50.
Dr. Alausa ya bayyana cewa, “Wannan ba tallafi ne kaɗai ba – wani dandalin baje koli ne ga sabbin haziƙai domin su jagoranci samar da sauyi a fannin masana’antu da fasahar Najeriya.”
Ita ma Ƙaramar Ministar Ilimi, Farfesa Suwaiba Sa’id Ahmad, ta ce “muhimmin jari ne ga tattalin arziƙin ilimi na ƙasar,” tana mai cewa shirin ya samo asali ne daga dogon nazari da shawarwari da aka yi da ɗalibai da shugabannin cibiyoyi.