Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Majalisar Wakilai Zata Kama Gwamnan Babban Bankin Najeriya Bisa Saɓa Dokokin Kula Da Kuɗaɗe

Kwamitocin haɗaka na Majalisar Wakilai kan Lissafin Kuɗi da Kadarorin Jama’a sun yi barazanar bayar da sammacin kama Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Olayemi Michael Cardoso, saboda ƙin bayyana a gabansu duk da gayyatar da aka yi masa sau da dama.

Shugabannin kwamitocin, Hon. Bamidele Salam da Hon. Ademorin Kuye, sun bayyana cewa yunƙurin rashin sa hannu da Gwamnan CBN ke yi ya saɓawa dokokin ƙasa kuma ya jefa binciken cikin matsala.

A cewar rahoton da Akanta Janar na Tarayya ya gabatar, Babban Bankin Najeriya na bin gwamnatin tarayya bashi da ya kai Naira tiriliyan 5.2 daga rarar kuɗaɗen da ya samu tsakanin 2016 zuwa 2022.

WANI LABARIN: Za A Fara Bayar Da Tallafin Naira Miliyan 50 Ga Ɗaliban Kimiyya Da Fasaha A Najeriya

Kwamitin ya ce bisa ga tanadin dokar Finance Act 2020, duk wata riba daga hannun jarin da ba ta da mai nema na tsawon shekaru shida, da kuɗaɗen da ke cikin asusun banki da ba a taɓa su ba, dole ne a tura su zuwa Unclaimed Funds Trust Fund ƙarƙashin kulawar Ministan Kuɗi da Hukumar Lamuni ta Tarayya.

Lauyan Gwamnatin Tarayya ya tabbatar da sahihancin dokar 2020, wanda hakan ya saɓawa matsayar CBN da ke jinginar da iko ga Financial Institutions Act.

Don haka kwamitin ya umurci CBN da ya biya Naira tiriliyan 3.64 cikin kwanaki 14 daga ranar 27 ga Yuni, 2025, yayin da sauran kuɗaɗen za a ci gaba da tantance su.

Sai dai har yanzu Gwamnan CBN bai cika wannan umarni ba, kuma bai bayyana a gaban kwamitin domin kare kansa ba, lamarin da ƴan majalisar suka ce ya saɓawa dokar kundin tsarin mulki da ƙa’idojin Majalisa na 1999 da aka sabunta.