Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Rikicin SDP Ya Ƙara Ta’azzara: NEC Ta Rushe Shugabancin Jam’iyya, Ta Ce Ba Ta San El-Rufa’i A Cikinta Ba

Jam’iyyar SDP ta sake fuskantar babban rikici yayin da kwamitin NEC na jam’iyyar ya rushe shugabancin Shehu Gabam, wanda ke a dakace, tare da naɗa sabbin shugabanni na wucin gadi domin ceto jam’iyyar.

Wannan mataki ya biyo bayan wani taron gaggawa da NEC ta gudanar a Abuja ƙarƙashin jagorancin Ibrahim Biu, inda ya bayyana cewa “yanzu an rushe kwamitin zartarwa na ƙasa.”

Sabbin shugabannin da aka naɗa sun haɗa da Adamu Modibo (shugaba), Abubakar Dogara (mataimaki), da Ekpeyong Ambo (sakataren jam’iyya), inda wasu suka ce an ɗauki matakin ne domin shawo kan rikicin cikin gida da ya durƙusad da jam’iyyar.

Sai dai Dr Olu Agunloye ya bayyana rushe kwamitin a matsayin na ba bisa ƙa’ida ba, yana mai cewa “taron NEC ɗin ba shi da inganci kuma ba a amince da shi daga kwamitin NWC ba.”

WANI LABARIN: ASUU Ta Yi Allah-wadai Da Sake Sunan Jami’ar Maiduguri, Ta Ce Za Ta Damfara Gwamnati A Kotu

Ibrahim Biu ya nuna takaicinsa kan yadda ƙoƙarin sulhu ya ci tura, yana mai cewa “rikicin ya haifar da rabuwar kai da tasiri a cikin jam’iyya tun bayan taron ƙarshe da aka yi a 2022.”

A gefe guda, SDP ta fice daga gamayyar jam’iyyun da Atiku Abubakar da ADC suka jagoranta, inda Dogara ya ce, “jam’iyyar ba za ta rasa asalinta ba, kuma za mu tsaya da ƙafafunmu a zaɓen 2027.”

A ƙarshe, jam’iyyar ta bayyana cewa ba ta da alaƙa da Nasir El-Rufai, inda ta bayyana cewa “ba mamba ba ne kuma ba shi da izini ko wata hujja da zai wakilci jam’iyyar ko magana a madadinta.”