Ma’aikatar Ilimi ta Tarayyar Najeriya ta ƙaryata rahotannin da ke cewa gwamnati ta sanya shekara 12 a matsayin mafi ƙarancin shekarun da ɗalibai za su iya fara ajin JSS1 a makarantu a faɗin ƙasar.
Cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Juma’a, mai magana da yawun ma’aikatar, Folasade Boriowo, ta ce “baki ɗayan rahoton ba daidai ba ne,” tana mai jaddada cewa babu wata sabuwar ƙa’ida da aka fitar da ke tabbatar da hakan.
Ta bayyana cewa “domin kore wani shakku, mafi ƙanƙantar shekarun shiga JSS1 yana nan a 10,” tare da ƙari da cewa bisa tsarin doka “babu yaron da zai kammala firamare a ƙasa da shekara 10.”
WANI LABARI: Kotu Ta Tura Shahararren Ɗan TikTok Gidan Yari Bisa Yaɗa Ƙaryar Tinubu Ya Mutu
Ma’aikatar ta ce rahoton da ke yawo bai samo asali daga kowace irin majiyar hukumar ba, kuma babu wani sabon tsari da ya musanya abin da ake amfani da shi a halin yanzu.
Duk da haka, sanarwar ta ce Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya tabbatar da cewa tsarin mafi ƙarancin shekaru kafin shiga jami’a a Najeriya yanzu haka yana nan a shekara 16.
Wannan na zuwa ne bayan rahotanni daga wasu jaridu sun nuna cewa gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da sabon tsarin da ya daidaita shekarun shiga JSS1 zuwa 12, musamman a makarantu masu zaman kansu.
A baya dai an samu saɓani tsakanin tsohon Minista, Prof. Tahir Mamman, da sabon Minista, Dr. Alausa, kan ko shekara 16 ko 18 ne mafi dacewa da ɗalibai su fara jami’a a Najeriya.