Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya bayyana farin ciki kan ƙulla yarjejeniya tsakanin Jami’ar Legas (UNILAG) da Jami’ar Birmingham, wata babbar jami’a a ƙungiyar Russell Group na Birtaniya.
Ya ce wannan haɗin gwiwa zai ƙarfafa bincike, karfafa koyar da STEMM, da faɗaɗa musayar ɗalibai da shirye-shiryen digiri biyu.
An kuma cimma matsaya kan horar da malamai da tallafawa ƙirƙire-ƙirƙire da shirye-shiryen samar da ayyukan yi.
Wakilan Jami’ar Birmingham, Cathy Gilbert da Charles Luke Wales, sun halarci taron tare da nuna jin daɗinsu na haɗa kai wajen inganta ilimi a Najeriya.
Dr. Alausa ya ce wannan shi ne karon farko da wata jami’a daga Russell Group za ta kafa tsarin ilimi a nahiyar Afirka.
“Kamar yadda Shugaba Bola Tinubu ya faɗa, matasa ne zuciyar wannan ƙasa,” in ji shi.
Ya bayyana cewa wannan haɗin gwiwa zai kawo ingantaccen ilimi kai tsaye gida domin ƙarfafa matasa.
Masu sharhi sun ce wannan yarjejeniya na iya zama babbar dama ga ɗalibai da malamai na Najeriya wajen samun ƙwarewa ta ƙasa da ƙasa ba tare da barin gida ba.
Wannan mataki ya kuma nuna yadda gwamnatin Tinubu ke ƙoƙarin yin tasiri kai tsaye a fannin ilimi duk da ƙalubalen tattalin arziƙin da ake fuskanta.