Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Sankara Ya Raba Naira Miliyan 50 Ga Matasa Da Mata 250 A Ƙaramar Hukumarsa

Daga: Mika’il Tsoho, Dutse

A ƙalla matasa da mata 250 a Jihar Jigawa sun amfana da tallafin kuɗi har Naira miliyan 50 daga Kwamishinan Harkokin Jin Ƙai da Ayyuka na Musamman, Hon. Auwal Sankara, a wani shirin ƙarfafa tattalin arziki da ya ƙaddamar a Ringim.

Kowane ɗaya daga cikin masu cin gajiyar ya samu Naira dubu 200, wanda Sankara ya bayyana a matsayin ƙoƙarin tallafa wa matasa da mata wajen farawa ko faɗaɗa kasuwancinsu.

“Wannan shiri nawa ne na ƙashin kai domin cike giɓi a cikin ƙoƙarin Gwamna Umar Namadi na samar da ayyukan yi da rage talauci,” in ji Sankara, wanda shi ma ɗan asalin Ringim ne.

Ya ce shirin zai taimaka wa wasu su faɗaɗa kasuwancin da suke yi, yayin da zai bai wa wasu damar fara sabuwar sana’a mai muhimmanci.

Gwamna Namadi, wanda ya halarci bikin ƙaddamarwar, ya yaba da wannan mataki, yana mai cewa ya yi daidai da manufofin ajandar sa mai ƙudiri 12 da ke nufin kawar da talauci da samar da cigaba.

“Magance talauci muhimmin mataki ne wajen hanzarta bunƙasar tattalin arziƙi da samar da ayyukan yi,” in ji Gwamnan.

Ya jaddada muhimmancin horas da matasa kan sana’o’i da kuma samar da ingantaccen yanayin kasuwanci domin cimma wannan buri.

Gwamnan ya yi kira ga ƴan siyasa, masu riƙe da muƙaman gwamnati, ƴan kasuwa da sauran masu kuɗi da su riƙa tallafawa jama’a domin gina al’umma mai ƙarfi.

Wannan tallafin, kamar yadda jama’a suka bayyana, na iya zama matakin farko wajen samar da cigaba mai ɗorewa a Jigawa.