Rundunar Ƴan Sanda a Jihar Kano ta yi kira mai ƙarfi ga masu keke Napep, musamman ƙananan yara, da kuma direbobi masu karya dokar fitilun kan hanya.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce ana samun “tuƙin ganganci” daga yara ƙananan yara, wanda ya haddasa haɗurra 16 a watan Agusta kawai, tare da raunata mutane da lalata dukiya.
Rundunar ta kuma nuna damuwa kan “raina” dokokin zirga-zirga, wanda ke janyo cunkoso da haɗurra.
“Tuƙa keke Napep ga yara ba daidai ba ne, kuma yana barazana ga rayuwar jama’a. Iyaye ku hana yaranku tuƙi, in ba haka ba ku fuskanci hukunci mai tsauri,” in ji sanarwar.
Kwamishinan Ƴan Sanda a jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ya buƙaci a bi doka, ya kuma gargaɗi masu karya dokoki da cewa za a kama su.
Rundunar ta ce ta tura jami’ai domin cafke masu laifi a duk fadin jihar.