Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Tinubu Ya Naɗa Sabbin Shugabanni A Hukumar NCC Da Asusun USPF

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana sababbin naɗe-naɗe a hukumar Nigerian Communications Commission (NCC) da Universal Service Provision Fund (USPF) domin ƙara inganta aikin fasahar sadarwa da isar da intanet a yankunan karkara.

Idris Olorunnimbe, wanda ya taɓa zama mamba a hukumar Lagos State Employment Trust Fund, ya zama sabon shugaban NCC, yayin da Dakta Aminu Maida zai ci gaba da jagoranci a matsayin babban jami’in zartarwa na hukumar.

Sauran membobin sun haɗa da Abraham Oshidami, Rimini Makama, Hajia Maryam Bayi, Kanal Abdulwahab Lawal mai ritaya, Sanata Lekan Mustafa, Chris Okorie, da Princess Oforitsenere Emiko tare da sakataren hukumar.

A ɓangaren USPF, Ministan Sadarwa, Fasaha, da Tattalin Arzikin Dijital, Dakta Bosun Tijani, shi ne shugaban kwamitin, yayin da Olorunnimbe ya zama mataimakin shugaba.

Mambobin USPF sun haɗa da wakilai daga ma’aikatun tarayya, ƴan kasuwa, da masana, ciki har da Uzoma Dozie, Peter Bankole, Abayomi Anthony Okanlawon, da Gafar Oluwasegun Quadri.

An kafa USPF ne domin tabbatar da an samu damar shigar da fasahar sadarwa a ko’ina, musamman a ƙauyuka da yankunan da ba su da isassun hanyoyin sadarwa.

Masu nazari na ganin cewa naɗe-naɗen na iya zama dama ga gwamnati wajen rufe giɓi tsakanin birane da karkara wajen samun damar intanet.

Gwamnati ta sha alwashin amfani da hukumar NCC da asusun USPF wajen ƙirƙirar ayyukan da zasu bunƙasa tattalin arziƙi, samar da ayyukan yi, da kuma inganta sadarwa a Najeriya.

Sai dai idan sababbin shugabannin ba su nuna gagarumin tasiri ba, ana iya ci gaba da fuskantar ƙalubalen da suka daɗe suna hana Najeriya cika burinta a fannin sadarwa.