Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Jam’iyyu A Kano Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya Kafin Zaɓen Cike Gurbin Ranar Asabar

Shugabannin jam’iyyun siyasa a jihar Kano sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya domin tabbatar da gudanar da zaɓukan cike gurbi cikin lumana a ranar Asabar, 16 ga Agusta 2025.

Kakakin rundunar ƴan sandan a jihar, SP Abdullahi Haruna, ya bayyana cewa an sanya hannun ne a taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a hedikwatar rundunar a Bompai.

Ya ce, “A shirin sake zaɓuka na mazabar Ghari/Tsanyawa da na cike gurbi na Bagwai/Shanono, rundunar ƴan sandan Kano ta kira taron haɗin gwiwa da ƴan takara da shugabannin jam’iyyu domin tabbatar da zaman lafiya da bin dokokin zaɓe.”

Kwamishinan ƴan sanda, Ibrahim Bakori ya gargaɗi shugabannin jam’iyyu da kada su karya ka’idojin da aka amince da su, yana mai cewa duk wani tashin hankalin da zai iya tasowa, za a ɗauki mataki a kansa cikin gaggawa.

“Mun ɗauki alƙawarin tura jami’an tsaro a duk faɗin yankunan da za a yi zaɓe don kare rayuka da dukiyoyi,” in ji shi.

Haka kuma ya buƙaci dukkan masu ruwa da tsaki su yi aiki tare da jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da nasarar zaɓen.

Yarjejeniyar ta jaddada cewa za a gudanar da kamfen da dukkan harkokin zaɓe cikin bin doka.

SP Haruna ya tabbatar da cewa rundunar ba za ta lamunci duk wani yunƙuri na tayar da tarzoma ba.