Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Tsoron Boko Harama Ya Sa Ɗaruruwan Ƴan Najeriya Tafiya Kamaru Domin Kwana A Kan Tituna

Ɗaruruwan mazauna Kirawa a jihar Borno da Boko Haram suka raba da muhallansu sun koka kan halin ƙuncin rayuwa, inda suka bayyana cewa suna kwana a Kamaru cikin tsoron hare-haren mayaƙa sannan su dawo Najeriya da safe.

Sun bayyana wa jaridar The PUNCH cewa bayan harin da aka kai ranar Asabar wanda ya tilasta sojoji barin garin, da dama daga cikinsu na kwana ne a tituna, masallatai da ɗakunan makarantu a ƙauyukan kan iyaka.

Hakimin Kirawa, Abdulrahman Abubakar, ya ce, “Ba mu ƙara samun irin wannan hari ba tun bayan dawowar mu garin shekaru da suka wuce, amma yanzu mutane na rayuwa tsakanin ƙasashe biyu cikin tsoro.”

Wani mazaunin garin, Buba Aji, ya ce, “A daren Litinin, ruwan sama ya yi tsanani, amma jama’a da dama sun kwana a cikin ruwan, wasu kuma a tituna, masallatai, da ɗakunan makarantu.”

Ya buƙaci a gaggauta dawo da sojojin Najeriya domin tabbatar da tsaro.

Wani mazaunin garin, Atahiru Lawan, ya ce kashi 80 zuwa 90 na jama’ar Kirawa sun tsere zuwa Kamaru ba tare da samun mafaka ba.

Sai dai kwamishinan tsaro na jihar, Janar Ishaq Abdullahi (rtd), ya ce gwamnatin jihar tana kan aiki don magance matsalar.

Shugaban ƙungiyar ci gaban Kirawa, Yakubu Mabba, ya ƙalubalanci iƙirarin rundunar sojin Najeriya da cewa ba a kai hari ga sojojinta ba, yana mai cewa, “A halin yanzu babu sojojin Najeriya a garinmu, muna dogaro ne da sojojin Kamaru.”