Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Farashin Bitcoin Ya Yi Mugun Hawa, Ya Wuce $124,000 Saboda Sabbin Dokokin Amurka

Farashin Bitcoin ya cimma sabon matsayi a safiyar yau Alhamis, inda ya zarce dala $124,000 a kasuwar Asiya, abin da ya jawo cece-kuce a tsakanin masu zuba jari.

Wannan hauhawa ta zo ne bayan ya kai dala $124,500 kafin ya ɗan sauka, ya zarce tsohuwar ƙololuwar da ya kai a watan Yulin da ya gabata.

Rahotanni sun nuna cewa ƙarin darajar hannayen jari a kasuwar Amurka, musamman a S&P 500 da Nasdaq, ya taimaka wajen tura farashin sama.

Babban mai nazarin kasuwannin kuɗi na XS.com, Samer Hasn, ya ce, “Kasuwar crypto tana cikin yanayi mai matuƙar kyau yanzu.”

Ya bayyana cewa shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump ya kawo sauye-sauyen dokoki da suka kawar da shingayen da suka hana bankuna hulɗa da kamfanonin crypto.

Hasn ya ƙara da cewa, “Trump na iya hanzarta haɗe cryptocurrencies da tsarin kuɗi na ƙasa, duba ga sha’awar shi da iyalinsa ga wannan fanni.”

Kamfanoni masu ƙarfi kamar Trump Media Group da Tesla na Elon Musk sun riga sun sayi Bitcoin mai tarin yawa, abin da ya ƙara ƙarfin kasuwa.

Wannan ci gaban ya sake tabbatar da cewa Bitcoin na ci gaba da zama jagora a harkar kuɗi ta zamani duk da tsauraran dokoki da ya sha fuskanta a baya.