Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Tinubu Zai Cire Tallafin Lantarki Gaba Ɗaya, Abin Da Zai Ninninka Farashinta Ga Ƴan Ƙasa

Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da shiri na gaggawa domin biyan bashin wutar lantarki na naira tiriliyan 4 tare da kawo ƙarshen tallafin lantarki saboda yanayin takura ta kasafin kuɗi da ƙarancin kuɗaden shiga na gwamnati, a cewar rahoton LEADERSHIP.

Ministan Kuɗi, Wale Edun, ya bayyana a Abuja cewa, manufar ita ce daidaita kuɗi da fifita muhimman sassa bayan raguwar kudaden shiga da ta biyo bayan faɗuwar farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya, yana nanata cewa gwamnati na tsuke bakin aljihu a manyan abubuwan kasafin kuɗi.

LEADERSHIP ta ce cire tallafin gaba ɗaya zai mayar da matsakaicin farashin wutar lantarki daga naira 66 kan kowanne kilowat zuwa naira 209, duk da cewa an ɗaga Band A a Afrilun 2024 zuwa naira 225 kan kowanne kilowat kafin daga bisani ya koma naira 209 kan kowanne kilowat a halin yanzu.

Har zuwa Yunin 2025, nauyin tallafin da gwamnati ke biya a fannin lantarki ya kai naira tiriliyan 1.186 wanda ba a biya ba har yanzu, yayin da bashin naira tiriliyan 4 da kamfanonin samar da wuta (GenCos) ke bin gwamnati ya haddasa mummunar matsalar kuɗi da ke barazanar ɗorewar sashen.

Edun ya bayyana shirin komawa tsarin biyan wuta na pay-as-you-go bayan an biya ragowar basussukan, inda ya ce: “Daga yanzu, za mu tabbatar an ƙara karɓar kuɗi, a koma tsarin pay-as-you-go wanda ba ya barin gwamnati ta sake sanya farashi.”

Ya ƙara da cewa ana nufin kawar da yarjejeniyoyin sayen wuta da ke ɗora nauyi a kan gwamnati: “Manufar ita ce a maye gurbinsu da masu zuba jari da ke samar da wuta su kuma sayar da ita, ba a rataya ta kan gwamnati ba,” in ji shi, kamar yadda LEADERSHIP ta ruwaito.

LEADERSHIP ta kuma ce karɓar kuɗaɗen shiga ya gaza hasashe saboda raunin ɓangaren mai da ba na mai ba, inda matsakaicin samar da ɗanyen mai a rabin farko na 2025 ya tsaya a ganga miliyan 1.67 a rana, yayin da ministan ya jaddada cewa ba a katsewar babban layin wutar lantarki a bana ba.

Masana sun yi jan kunne kan tasirin cire tallafin lantarkin: Daraktan CPPE, Dr Muda Yusuf, ya yabawa yiwuwar samun wuta mai ɗorewa inda ya ce, “Ƙananan masana’antu za su rage dogaro da dizal da fetur,” amma ya ƙara da cewa “farashin wuta zai matuƙar tashi”.

Shima shugaban ASBON, Dr Femi Egbesola, ya gargaɗi cewa ƙarin farashin “zai ƙara wa ƙananan masana’antu nauyi” tare da kira da cewa “muna ƙarfafa bayar da tallafi da tallafin da aka nufa da kyau ga ƙananan masana’antu”.

Shi kuma Babban Masanin Tattalin Arziki na SPM, Dr Paul Alaje, wanda ya ce “da farko farashin makamashi zai tashi, hauhawar farashi kuma za ta ƙaru,” yana roƙon a cire tallafin a hankali tare da samar da kariya ga masu rauni.