Daga: Mika’il Tsoho, Dutse
Ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, ya fito da sanarwa yana ƙaryata rahotannin da ke cewa APC ta faɗi a akwatin zaɓensa na Babura Kofar Arewa Polling Unit 001 a zaɓen cike-gurbi na Garki/Babura.
A cewar mai taimaka masa kan yaɗa labarai, Mati Ali, labarin “ba gaskiya ba ne, ƙarya ce tsagwaronta, kuma aiki ne na masu fitina da ke son ɓata sunan ministan.”
Sanarwar ta ƙara da cewa, “Domin kawar da shakku, akwatin ministan na gaskiya shi ne Babura Kofar Arewa Primary School Polling Unit 002, inda ya kaɗa ƙuri’arsa da kansa.”
Bisa ga sakamakon hukuma, APC ta samu ƙuri’u 188, PDP kuma ta samu ƙuri’u 164, wanda ya tabbatar da nasarar APC a akwatin ministan.
“Wannan sakamakon hukuma ya tabbatar da cewa mai girma Ministan ya yi nasara a akwatinsa a fili da kuma a bayyane,” in ji sanarwar.
Haka kuma, “An tabbatar da wannan sakamako ta hannun jami’in bayyana sakamako na INEC,” wanda ya tabbatar da ingancin nasarar jam’iyyar APC.
Ministan ya buƙaci jama’a da kafafen yaɗa labarai da su yi watsi da labaran ƙarya, tare da dogaro ga sakamakon da INEC ta fitar kawai.