Gwamnan jihar Jigawa, Mallam Namadi Umar, a wata tattaunawa PUNCH, ya ce gwamnatinsa ta fara manyan gyare-gyare bayan gudanar da cikakken bincike na asali (baseline survey), inda ya jaddada cewa, “Ba tare da samun bayanai ba, shugabanci zato ne; ba ma so mu yi aiki cikin jahilci”.
Ta haka aka tsara kuma aka fara aiwatar da manufofin ’12-point agenda’ da suka shafi ilimi, lafiya, noma, tattalin arziki, ruwa, muhalli da tsaro na zamantakewa, kuma gwamnan ya ce ana ganin sakamako mai kyau a wurare da dama.
Gwamnatin ta mai da hankali kan ƙara samun kuɗaɗen shiga na cikin gida (IGR), inda yanzu Jigawa ke nuna samun ci gaba bayan kasancewa ɗaya daga cikin jahohin da ke ƙasa a baya.
A fannin noma an magance matsalolin farashin taki, raunin aiyukan faɗakarwa da ƙarancin injuna ta hanyar samar da tsarin rarraba taki na gaskiya da kafa Jigawa State Farm Mechanisation Company don bai wa manoma injuna a rangwamen farashi.
Gwamnan ya jaddada ci gaba da faɗaɗa yawan gonaki daga hekta 60,000–70,000 a shekarun baya zuwa fiye da hekta 200,000 a 2020, 220,000 a 2024, da sama da hekta 300,000 a 2025, tare da burin cewa “zuwa 2030 Jigawa za ta samar da 50% na bukatun shinkafar Najeriya, Insha’Allah”.
An kafa cibiyoyin wayar da kai da kulawa guda 60 a faɗin jihar, kowanne da tarakta 10, injunan casa 2 da sauran kayan aikin noma da na’urorin GPS don lura, yayin da tsarin yin rajista yake ta hanyar yanar gizo da malaman gona na gida don manoma marasa ilimin fasaha.
Masu nazari sun ce idan aka ɗore da irin waɗannan manufofi da kulawa, Jigawa na da damar zama cibiyar juyin juya halin noma a Najeriya, amma sun jaddada cewa ɗorewa da ingantaccen shugabanci sune mabuɗin nasara.