
Daga: Badamasi Hamza Farin Dutse
A safiyar Litinin 18/08/2025 Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya jagoranci rantsar da Hon. Abdulkarim Musa Fagam a matsayin sabon shugaban ƙaramar hukumar Gwaram tare da Nasiru Zubairu Sara a matsayin mataimakinsa a zauren majalisar zartaswa da ke fadar gwamnan a Dutse.
Hon. Abdulkarim wanda kafin wannan muƙami ya riƙe matsayin mataimakin shugaban ƙaramar hukumar, inda a yanzu ya karɓi ragamar aikin bayan asalin shugaban, Farfesa Salim Abdurrahman Lawan, ya samu naɗi a matsayin kwamishinan sabuwar ma’aikatar haɓaka kiwon dabbobi ta jihar.
A jawabin da ya yi wa sabbin shugabannin, gwamnan ya ja kunnensu da cewa, su “yi adalci, su mutunta haƙƙokin jama’a, su haɗa kai kuma su guji duk wani abu da zai kawo rikici ko ruɗani a cikin al’umma”.
Gwamnan ya kuma jaddada cewa jam’iyyar APC ɗaya ce, don haka ya umurci shugabannin da su rungumi kowa da kowa a matsayin shugabanni tare da mai da hankali wajen aiwatar da ayyukan ci gaban al’umma.
Daga ƙarshe gwamnan ya tunatar da su cewa “mulki amanar Allah ne”, yana mai cewa saboda haka su gudanar da shi cikin gaskiya, adalci da haɗin kan jama’a domin tabbatar da kyakkyawan shugabanci.
An sanar da wannan rantsarwa ne ta hannun Malam Garba Al-Hadejawy, Special Assistant to the Governor (New Media), wanda ya sanya hannu a sanarwar ranar 18/08/2025.
Mazauna yankin sun nuna fatan cewa sabbin shugabannin za su bi umarnin gwamna, su mayar da hankali kan ayyukan raya ƙasa, zaman lafiya da bunƙasa rayuwar al’umma.