Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

JIGAWA: An Fara Tantance Almajirai Don Ba Su Horo Da Rubuta Jarrabawar NBAIS

An kammala sa-ido kan yadda aka gudanar da zaɓen almajiran tsangaya da malamai masu horaswa a Cibiyar Hadejia (Jigawa Arewa maso Gabas), wani muhimmin mataki da Hukumar Ilimin Tsangaya ta Jihar Jigawa ta shirya a cibiyoyi uku a faɗin jihar.

Manufar shirin ita ce “zaɓen rukuni na farko na masu haddar Al-Qur’ani” da za su samu horo na watanni shida cikin tsanaki, domin su cancanci rubuta jarrabawar NBAIS bayan kammalawa.

A cewar Mohammed T. Mohammed, Mai Ba wa Gwamnan Jigawa Shawara kan harkokin Tsangaya, shirin na Hukumar Tsangaya ya samu cikakken goyon bayan Gwamna Malam Umar Namadi, inda ya jaddada cewa yana daga cikin “Manufofin Gwamnati guda 12” da ke kare damar samun ilimi ga kowa da haɓaka rayuwar matasa.

Gwamnati ta ɗauki nauyin “dukkan kuɗin gudanar da horon da kuɗin zana jarrabawar NBAIS,” tare da masauki da “alawus na wata-wata” ga duk ɗaliban da suka samu gurbi a cibiyoyin da aka ware.

Rahoton sa-idon da Mohammed T. Mohammed ya fitar, ya tabbatar da cewa komai ya gudana “cikin tsari da kwanciyar hankali,” inda aka yi kira ga ɗalibai da malamai su ɗauki shirin “da muhimmanci matuƙa da kishin ci gaba.”

Masu ruwa da tsaki sun ce wannan tsari zai ba da gudummawa wajen ƙarfafa ilimin addini da fasaha ga matasa a Jigawa, musamman a yankunan karkara.

A cewar mai ba wa Gwamnan shawara, “an gudanar da zaɓar waɗanda za su mori shirin cikin nasara da bin ƙa’ida.”