Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

PDP Ta Ce Wa Wike Ya Fice Daga Cikinta Idan Ba Zai Bi Ƙa’idojinta Ba

Jam’iyyar PDP ta yi gargaɗi cewa za ta hukunta duk wani mamba da ya karya kundinta bayan maganganun Ministan Abuja, Nyesom Wike.

Wike a wani shirin talabijin ya ce “ban san wani babban taron ƙasa ba,” kuma “ba za mu yarda da ‘rashin adalci’ ba.”

Ya tambayi dalilin rashin sanar da shi zaman kwamatin NEC na jam’iyyar, yana mai cewa zai ƙalubalanci tsarin idan ya zama dole.

Kakakin PDP, Debo Ologunagba, ya ƙaryata shi, yana mai cewa “an kira NEC yadda doka ta tanada, an aika sanarwa, an kuma sanar da INEC.”

Ya tabbatar da cewa taron zai gudana a Ibadan ranar 15 zuwa 16 ga Nuwamba, 2025, tare da sauran shirye-shiryen da ke kan tsari.

Ologunagba ya ja kunnen masu bijirewa da cewa “yin jam’iyya ra’ayi ne, shigowa da fita kyauta ne, amma duk wanda ya tsaya a ciki to dole ya bi ƙa’ida.”

Rikicin ya sake hura wutar rikici a PDP yayin da shugabanci ke ƙoƙarin tsare doka da oda kafin babban taron.