Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

NELFUND Ya Fitar Da Sabon Tsarin Biyan Kuɗin Kula Da Kai A Makaranta ‘Upkeep Allowance’

Asusun Bayar da Bashin Karatu na Najeriya (NELFUND) ya sanar da dakatar da biyan kuɗin kula da kai na ɗalibai a lokacin da ake hutu.

Banda kuɗaɗen da ake biya kai tsaye ga makarantu, masu amfana na karɓar ₦20,000 a wata ne a tsawon zangon karatu a matsayin kuɗin kula da kai.

A cikin sanarwar, Oseyemi Oluwatuyi ya ce “kuɗin kula da kai za a taƙaita shi zuwa iya lokacin zangon karatu na kowacce makaranta kaɗai.”

Ya ƙara da cewa “da zarar an kammala shekarar karatu, biyan kuɗin kula da kai na wata-wata na wannan zangon nan zai tsaya nan take.”

NELFUND ta buƙaci ɗalibai su dinga sake nema a farkon kowanne zangon karatu domin su cancanci dukkan haƙƙoƙinsu.

Hukumar na sabunta dandalin bayar da bashin don tabbatar da gaskiya inda za a nuna kuɗin da ɗalibi ya karɓa a zangon da ya gabata.

A ranar 21 ga Agusta, 2025, NELFUND ta ce an raba kimanin naira biliyan 86 ga ɗalibai 449,039 a faɗin ƙasar nan.