Sanata Ahmed Wadada mai wakiltar Nasarawa ta Yamma ya shaida ficewa daga jam’iyyar Social Democratic Party (SDP).
A wata wasiƙa da ya aika wa Shugaban SDP a Tudun Kofa, Wadada ya ce ya bar jam’iyyar ne “sakamakon rikice-rikicen cikin gida.”
Ya rubuta, “na yanke shawarar barin SDP nan take saboda rabuwar kai da shari’o’i da suka addabi jam’iyyar.”
An zaɓe shi sanata a 2023 a matsayin ɗan jam’iyyar SDP bayan ya taɓa zama ɗan majalisar ƙarƙashin PDP.
Wadada bai bayyana jam’iyya ta gaba da zai shiga ba amma akwai hasashen zai iya komawa APC bayan ziyararsa ga Shugaba Bola Tinubu.
Ficewarsa ta rage adadin ƴan SDP a Majalisar Dattawa zuwa mutum ɗaya kacal.
Masu nazarin siyasa sun ce wannan sabon rikici na ƙara ba da dama ga APC wajen ci gaba da yin rinjaye a majalisa.