Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

A Najeriya Farashin Litar Man Fetur Ya Fi Tsada A Jihar JIGAWA, In Ji NBS

Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta ce a rahoton ta na “Premium Motor Spirit (Petrol) Price Watch” da aka fitar ranar Alhamis, farashin man fetur ya kasance a matsakaicin farashi na naira 1,024.99 a Yuli daga naira 1,037.66 a Yuni, inda ya fi tsada a Jigawa, Lagos da Sokoto.

A cewar rahoton, Jigawa ta fi kowacce jiha tsadar fetur inda aka sayar da shi a kan naira 1,107.52 a matsakaicin farashi, yayin da a Lagos ya kai naira 1,100.29 duk da kasancewarta cibiyar tashar jiragen ruwa, manyan tankoki da masana’antar Dangote.

A Sokoto farashin ya tsaya a naira 1,100.00, yayin da a Zamfara yake a naira 884.63, Yobe a naira 950.60 sai kuma Kogi a naira 986.67 a matsayin jihohin da suka fi rahusa a wannan lokaci.

NBS ta ce wannan “na nuna farashin na ci gaba da banbanta tsakanin jihohi” duk da ƙoƙarin da ake yi don daidaita kasuwar man fetur ɗin.

A shekara zuwa shekara, matsakaicin farashin litar man fetur ya tashi daga naira 770.54 a Yulin 2024 zuwa naira 1,024.99 a Yulin 2025, tare da kasancewar Arewa maso Yamma a matsayin wadda tafi tsada da naira 1,035.85, Arewa maso Gabas kuma ta kasance da mafi rahusa a naira 1,017.65.

Jaridar ICIR ta lura da cewa duk da faɗuwar ɗanyen farashin mai daga dala 85.15 kan kowacce ganga a Yulin 2024 zuwa dala 71.04 kan kowacce ganga a Yulin 2025, “ba a ga sauƙi a siyar da man ga ƴan ƙasa.”

Tun bayan cire tallafin man fetur a ranar 29 ga Mayun 2023, farashin litar ya tashi daga kusan naira 190 zuwa sama da naira 1,000, abin da ya ƙara hauhawar farashi da raɗaɗin rayuwa ga jama’a da dama a Arewa.