Hukumar yanayi ta Najeriya (NiMet) ta fitar da hasashen yanayi na ranar Asabar 23 ga Agusta 2025, tana jan hankalin al’umma musamman a yankunan Arewa kan yiwuwar samun guguwa tare da ruwan sama.
A cikin sanarwar da ta fitar a ranar 22 ga Agusta, hukumar ta ce, “Ana sa ran samun guguwa tare da matsaikacin ruwan sama a wasu sassan Borno, Yobe, Jigawa, Gombe, Bauchi, Adamawa, Taraba, da Kaduna.”
NiMet ta ƙara da cewa da yamma ana sa ran samun guguwa a wasu yankuna ciki har da Kano da Kebbi, yayin da yankin tsakiyar kasar zai fuskanci sassauƙan ruwan sama a wasu lokuta.
A kudancin ƙasar kuma ana has ashen samun gajimare da yiwuwar ruwan sama lokaci-lokaci wanda zai shafi jihohi da dama.
Hukumar ta yi gargaɗi da cewa, “Ana ba wa mazauna yankuna masu barazanar ambaliya shawara da su ɗauki matakan kariya da suka dace.”
An kuma buƙaci hukumomin yankuna, jami’an bayar da agaji da sauran masu ruwa da tsaki su kasance cikin shiri don rage illar ambaliya idan ta faru.
Ana kira ga manoma, matafiya da ƴan kasuwa su bi shawarwarin NiMet kafin tafiye-tafiye ko yin manyan ayyuka.
