Hukumar NAFDAC ta fitar da sanarwa tana gargaɗin jama’a game da yaɗuwar madarar sachet ta Cowbell “Our Milk” mai nauyin 12g da aka tabbatar cewa ta bogi ce kuma ana sayar da ita a faɗin ƙasar.
Kamfanin Promasidor Nigeria Ltd, mai lasisin samar da samfurin, ya shaidawa hukumar cewa tsohon gidan madarar mai “Our Milk” an daina amfani da shi tun Satumbar 2023, kuma “ba a buga shi ko rarraba shi ba.”
NAFDAC ta jaddada bambance-bambance na zanen gidan madarar da tsakanin na gaskiya da na bogin.
Ta yi nuni da cewa, na bogin ba a buga shi da kyau ba, bugun leda wato laser printing saɓanin na bogin da aka yi da tawada.
NAFDAC ta yi gargaɗi cewa amfani ko shan madarar bogin na iya zama barazana ga lafiya da tsaro, don haka jami’ai da masu sayarwa su kula sosai.
Hukumar ta umurci daraktocin yankuna da wakilai a jihohi su gudanar da bincike, su tattara kayayyakin da ba na ƙa’ida ba kuma ta roƙi masu saye suna siyan kayan abinci daga masu lasisin hukumar.
Don bada rahoto kan wani abu da ke faruwa, NAFDAC ta ba wa jama’a lambar waya: 0800-162-3322 da imel: mailto:sf.alert@nafdac.gov.ng.