Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

ACF Ta Ce Babu Ruwanta Da Wata Jam’iyya, Hankalinta Na Kan Ceto Arewa Ne Kawai

Arewa Consultative Forum (ACF) ta sake tabbatar da cewa ba ta da wata jam’iyya, ta mai da hankalinta ne ga ceto Arewa da muradun al’ummarta ba wai ga kowace jam’iyya ba.

Shugaban ACF, Chief Mamman Mike Osuman (SAN) ne ya bayyana hakan a Kaduna yayin taron shugabannin ƙungiyar karo na 78.

Ya yi gargaɗin cewa kodayake mambobi na da ra’ayoyinsu na ƙashin ƙansu, “ACF ba jam’iyya ba ce; muna tsantseni, ba mu haɗa kai da kowace jam’iyya ba, amma muna, cikin tsananin yarda, ba tare da nadama ba, cikin nuna kishi’ a kan aikin ceton Arewa da mutanenta ba tare da saɓa ƙa’idar kasancewar Najeriya dunƙulalliyar ƙasa ba.”

Ya ce, za su ci gaba da aiki tare da ƙungiyoyin da ke da irin wannan manufa, inda ya bayyana gayyatar ƙungiyar Forum for National Restoration don yi wa mambobi bayani a taron.

Osuman ya buƙaci shugabanni da jama’ar Arewa su kasance a faɗake kan tsaro, makirci da bala’o’i, yana jaddada cewa “ba lokaci ba ne na ɓoye kai a ƙasa ko zaman shiru.”

Daga ƙarshe ya ja kunnen mambobi kan yaɗa ra’ayoyi marasa tabbas a dandalin Rapid Response, ya kuma ce “mu rungumi ƴan’uwantaka, gaskiya da bin doka,” tare da sanar da shirye-shiryen bikin cika shekaru 25 na ACF a tsakiyar watan Oktoba, 2025.