Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

ADC Na Ci Gaba Da Karɓar Jiga-Jigan PDP A Jihohin Arewa Maso Gabas

Rahotanni daga jihohin Adamawa, Yobe da Gombe na nuna cewa haɗakar jam’iyyar ADC ta ƴan hamayya na ci gaba da karɓe manyan mambobi daga jam’iyyar PDP, ciki har da shugabanni na ƙananan hukumomi da tsoffin masu riƙe da muƙamai a jihohi.

A Adamawa, Hon. Umar Jada ya bayyana cewa “shugaban PDP a ƙaramar hukumar Girei da mataimakinsa da sauran shugabanni goma sun ajiye muƙamansu sun koma ADC,” yana mai cewa haɗin gwiwar nan da ƴan adawa ke jagoranta zai ƙara karfi a makonni masu zuwa.

A jihar Yobe kuwa, tsohon jagoran PDP, Adamu Maina Waziri ya tabbatar da cewa “akwai shugabannin jam’iyyar PDP da suka yi murabus daga muƙamansu kuma sun koma ADC bayan taron da wakilai daga ƙananan hukumomi 17 suka halarta.”

WANI LABARIN: Akwai Matuƙar Ƙarancin Malamai A Makarantun Firamaren Najeriya – UBEC

Wannan sauyin sheƙar na zuwa ne yayin da ADC ke zargin wasu jami’an gwamnati daga jam’iyyar APC da ƙoƙarin tarwatsa shirin haɗin guiwar da suke yi ta hanyar kiran wasu manyan shugabanni zuwa tarukan sirri.

Duk da haka, jam’iyyar PDP ta bayyana cewa ba ta damu da ficewar waɗanda ta kira “ƴan tsiraru” ba, inda Ibrahim Abdullahi, mataimakin mai magana da yawunta, ya ce: “ba abin mamaki bane su tafi, musamman idan madugunsu ne ya sauya sheƙa.”

A cewarsa, duk da cewa an samu sauyin sheƙa a wasu sassan Arewa maso Gabas, “ba mu damu ba, ko a jikinmu, domin a wasu yankuna kamar Sokoto ko Arewa ta Tsakiya ba wanda ya damu da taronsu.”

Sai dai har yanzu jam’iyyar APC mai mulki ba ta fitar da wata sanarwa ba kan zargin da ADC ta yi mata.